Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Argentina, Lionel Messi, ya bayyana ban kwanarsa da tawagar ƙasar a matsayin “ranar da ta fi baƙanta min rai a rayuwata”, bayan ya buga wasansa na ƙarshe da Argentina.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Messi ya bayyana hakan ne bayan wasan sada zumunci da Argentina ta doke Benin da ci 3-0 a filin wasa na Monumental da ke Buenos Aires ranar Talata.
Messi ya taka muhimmiyar rawa a wasan, inda ya ci ɗaya daga cikin ƙwallayen Argentina sannan ya taimaka aka zura wasu biyu, yayin da dubban magoya baya suka halarci filin domin yi masa bankwana bayan shafe shekaru 21 yana wakiltar ƙasar.
Bayan kammala wasan, Messi ya fito gaban magoya baya, inda ya bayyana farin cikinsa da kasancewa cikin tawagar Argentina na tsawon fiye da shekaru 20.
Ya ce wakiltar Argentina ya kasance babban abin alfahari a gare shi, yana mai cewa ko a lokacin da abubuwa suka kasance masu wahala, bai taɓa daina ƙoƙarin kasancewa tare da tawagar ƙasar ba.
Messi ya ce zai ji matuƙar ciwo saboda ba zai ƙara fitowa wasa da rigar Argentina ba, yana mai cewa da a ce zai iya, zai ci gaba da buga wa ƙasar wasa har tsawon rayuwarsa.
Ya bayyana cewa buga wa tawagar Argentina wasa shi ne ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi kyau da suka taɓa faruwa a rayuwarsa.
Dan wasan mai shekaru 39 ya kuma bayyana cewa komawarsa filin wasa na Monumental domin yin bankwana ya kasance abin farin ciki da kuma baƙin ciki a lokaci guda, musamman saboda muhimmancin wurin a tarihin ƙwallon ƙafarsa da na Argentina.
Messi ya ce yanzu zai koma gefe tare da sauran magoya baya domin ci gaba da mara wa tawagar Argentina baya, yana mai kira ga kowa da kowa da ya ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai.
Ritayar tasa ta kawo ƙarshen shekaru 21 na rayuwarsa a tawagar Argentina, inda ya zama ɗan wasan da ya fi kowa buga wa ƙasar wasanni, tare da kuma kasancewa wanda ya fi kowa zura mata ƙwallaye.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa ya kammala aikinsa da wasanni 208 da ƙwallaye 126.
A lokacin da yake wakiltar Argentina, Messi ya taimaka wa ƙasar ta lashe manyan kofuna, ciki har da Copa América da Kofin Duniya na 2022, lamarin da ya ƙara tabbatar da muhimmancinsa a tarihin tawagar ƙasar.
Bankwanarsa ta zo ne bayan Argentina ta kai wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2026, inda ta sha kashi a hannun Spain.
Messi ya ce abubuwan da suka faru a wannan gasar sun yi matuƙar tasiri a jikinsa da kuma zuciyarsa.
A wasansa na ƙarshe, Argentina ta doke Benin da ci 3-0, inda Messi ya taka rawa kai tsaye a dukkan ƙwallayen da aka zura, ciki har da ci da ya zura daga bugun fanareti.
Fiye da magoya baya 85,000 ne suka cika filin wasa na Monumental domin ganin ɗan wasan ya yi bankwana da tawagar ƙasar, a wani biki da ya haɗa da yabo da nuna godiya ga irin gudunmawar da ya bayar ga ƙwallon ƙafar Argentina.
Haka kuma, ’yan wasa da tsofaffin abokan wasansa daga sassa daban-daban na duniya sun yi ta aika saƙonnin yabo da girmamawa gare shi, yayin da aka yaba masa kan irin tasirin da ya yi a ƙwallon ƙafa da kuma tarihin Argentina.
