DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 7, 2026
HomeKetareGhana ta fara neman shiga BRICS, ƙungiyar da Nijeriya ke cikinta

Ghana ta fara neman shiga BRICS, ƙungiyar da Nijeriya ke cikinta

Gwamnatin Ghana ta amince da fara shirin neman shiga ƙungiyar ƙasashe masu tasowa ta BRICS, domin faɗaɗa dangantakarta da sauran ƙasashe da kuma ƙara samun damarmaki na bunƙasa tattalin arzikinta.

TRT Afrika ta ruwaito cewa ministan harkokin wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, ne ya bayyana hakan a Accra ranar Talata, bayan majalisar ministocin gwamnatin Shugaba John Dramani Mahama ta amince da matakin.

Ablakwa ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Mahama na faɗaɗa abokan hulɗar Ghana a duniya, musamman wajen jawo jarin ƙasashen waje, bunƙasa kasuwanci da samar da ƙarin damarmaki ga tattalin arzikin ƙasar.

Ministan ya ce shiga BRICS ba zai maye gurbin dangantakar Ghana da abokan hulɗartar ba ciki har da asusun ba da lamuni na duniya (IMF) da bankin duniya, sai dai zai ƙara wa ƙasar wasu zaɓuɓɓuka wajen samun haɗin gwiwa da damar ci gaba.

A cewarsa, Ghana na son samun ƙarin abokan hulɗa a fannin tattalin arziki, musamman ƙasashen da za su taimaka mata wajen samar da ayyukan yi, jawo masu zuba jari a waje da bunƙasa masana’antu.

Ablakwa ya bayyana Indiya, Brazil da China a matsayin wasu daga cikin muhimman ƙasashen da Ghana ke da sha’awar ƙarfafa hulɗa da su, yana mai bayar da misalin yadda kasuwanci tsakanin Ghana da Indiya ya ƙaru daga kusan dala biliyan uku a shekarar 2024 zuwa kusan dala biliyan bakwai.

Ya ce gwamnatin Ghana tana shirya gabatar da takardar neman shiga ƙungiyar a hukumance, sannan za ta nemi goyon bayan ƙasashen da suke cikin BRICS.

Ministan ya kuma bayyana cewa Ghana ta nemi goyon bayan Indiya kan yunkurinta na shiga ƙungiyar, yayin da ministan harkokin wajen Indiya, Subrahmanyam Jaishankar, ya bayyana cewa ƙasarsa tana goyon bayan burin Ghana, sai dai ya ce batun kasancewa mamba na buƙatar shawarar sauran ƙasashen BRICS.

Ablakwa ya ce gwamnatin Ghana na son ƙasar ta ƙara samun ikon sarrafa albarkatun da take da su, maimakon ci gaba da fitar da albarkatun ƙasa ba tare da ƙara musu ƙima a cikin gida ba.

Ya ce gwamnatin Mahama na kallon ƙarin haɗin gwiwar ƙasashen duniya a matsayin wata hanya ta tallafa wa shirin sauya tsarin tattalin arzikin Ghana, ƙara masana’antu da samar da ayyukan yi.

BRICS ta samo asali ne daga ƙungiyar BRIC, wadda Brazil, Rasha, Indiya da China suka kafa, kafin a ƙara Afirka ta Kudu a shekarar 2011.

Daga baya ƙungiyar ta faɗaɗa zuwa wasu ƙasashe.

A halin yanzu, BRICS na da cikakkun mambobi 11, waɗanda suka haɗa da Brazil, China, Masar, Habasha, Indiya, Indonesia, Iran, Rasha, Saudi Arabia, Afirka ta Kudu da Hadaddiyar Daular Larabawa Dubai.

A shekarar 2025 kuma, Nijeriya na cikin ƙasashen da suka shiga BRICS a matsayin ƙasar abokiyar hulɗa, tare da Belarus, Bolivia, Kazakhstan, Cuba, Malaysia, Thailand, Uganda, Uzbekistan da Vietnam.

BRICS na samar da wani dandali da ƙasashe mambobi da abokan hulɗa ke amfani da shi wajen tattauna batutuwan tattalin arziki da siyasa na duniya da na yankuna, ciki har da sake fasalin wasu cibiyoyin gudanar da harkokin duniya.

Idan Ghana ta kammala shirin neman shiga BRICS, hakan zai ƙara faɗaɗa hulɗar ƙasar da ƙasashen da ke cikin ƙungiyar, musamman a fannonin kasuwanci, zuba jari, masana’antu da ci gaban tattalin arziki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata