DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiGwamnonin Arewa maso Yamma ba za su yi sulhu da ‘yan bindiga...

Gwamnonin Arewa maso Yamma ba za su yi sulhu da ‘yan bindiga ba – Gwamna Aliyu

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa gwamnonin yankin Arewa maso Yamma ba za su shiga wata tattaunawar sulhu da ‘yan bindiga ba, yana mai jaddada kudirin gwamnatocin yankin na kawo karshen matsalar tsaro da ke addabar al’ummarsu.

Kamar yadda sanarwar da Darakta Janar na yaɗa labarai na gwamnan, Abubakar Bawa, ya fitar ta nuna, gwamnan ya bayyana hakan ne a Jihar Katsina yayin ƙaddamar da titin Yandaki–Shinkafi–Kofar Sauri mai tsawon kilomita 8.1.

Ya ce gwamnonin yankin sun hada kai wajen yakar matsalar tsaro, tare da nuna cewa gwamnatoci suna zuba manyan kudade da sauran kayan aiki domin dakile ayyukan ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.

A cewarsa, ba za a taba amincewa da duk wata yarjejeniya da masu aikata laifi ba, sai dai idan sun mika wuya ba tare da wani sharadi ba.

Ahmed Aliyu ya kuma tabbatar wa al’ummar yankin cewa gwamnatoci tare da hadin gwiwar jami’an tsaro suna sake tsara hanyoyin da za su kawo karshen matsalar ‘yan bindiga da sauran nau’o’in laifuka a yankin.

Ya bukaci al’umma da su hada kai da gwamnati da jami’an tsaro ta hanyar tona asirin masu ba ‘yan bindiga bayanai a cikin al’umma, yana mai cewa babu wani hari da ‘yan bindiga ke kai wa ba tare da samun taimako daga cikin gida ba.

Haka kuma, gwamnan ya shawarci jama’a da su kasance masu lura da duk wani motsi na mutane da ba su amince da su ba, domin taimakawa wajen dakile hare-haren ‘yan bindiga.

Gwamnan ya yaba wa Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, bisa jagorancin da yake bayarwa da kuma kokarinsa na kafa rundunar tsaron al’umma ta jihar domin taimakawa hukumomin tsaro wajen yakar ‘yan bindiga.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata