DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeLabaraiMURIC ta zargi Tinubu da fifita kiristoci kan musulmi

MURIC ta zargi Tinubu da fifita kiristoci kan musulmi

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta MURIC ta zargi Gwamnatin Tarayya da nuna wariya, bayan fara gina wani babban coci da cibiyar aikin hajji ta Kirista a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja kan kuɗin naira biliyan 25.

Kamar yadda sanarwar da Daraktan ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar ta nuna, ya ce gwamnatin tare da Ƙungiyar Kiristoci ta CAN ne suka ƙaddamar da aikin, yana mai tambayar dalilin fifita wani bangare.

Akintola ya kuma soki bai wa waɗanda rikici ya shafa a Jihar Filato tallafin naira biliyan 2, yana mai cewa ba a ba wa waɗanda suka fuskanci irin wannan matsala a jihohin Borno, Sokoto, Zamfara, Kebbi da Kwara irin wannan tallafi ba.

Ya ce hakan ya jawo cece-kuce a tsakanin Musulmi, inda ya kara da cewa ana ganin tsarin ba ya da daidaito.

Hakazalika, ya yi zargin cewa an bayar da naira biliyan 1.2 ga jihohin Arewa 19 domin bikin Eid-el-Kabir, yana mai tambayar dalilin da ya sa aka ba jiha guda biliyan 2, amma sauran jihohi da dama suka raba biliyan 1.2.

MURIC ta bukaci gwamnatin tarayya ta bayyana lokacin da za ta ba Musulmi fili da kuɗi domin gina babban masallacin ƙasa, tana mai cewa dole ne a samu adalci tsakanin addinai.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata