Ministan Tsaron Nijeriya, Bello Matawalle, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu har yanzu yana da ƙarfi a siyasance a yankin Arewa maso Yamma, kuma yana da kyakkyawar damar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Matawalle ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ahmad Dan-Wudil, ya fitar a Kaduna ranar Alhamis.
Ya ce babu wata farfaganda, yaɗa ƙarya ko hare-haren siyasa daga jam’iyyun adawa da za su hana Shugaba Tinubu ci gaba da aiwatar da manufofinsa ga al’ummar Najeriya.
Ministan ya zargi wasu ‘yan adawa musamman a Arewa maso Yamma da ƙoƙarin yaɗa bayanan da ba su dace ba tare da nuna matsalolin tsaro fiye da yadda suke domin rage darajar nasarorin da gwamnatin Tinubu ke samu.
A cewarsa, masu sukar gwamnati ba sa son amincewa da ci gaban da ake samu wajen yaƙi da ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro, musamman a jihohin Zamfara, Sokoto, Katsina, Kaduna da Kebbi.
Jaridar Daily Nigerian ta kuma ruwaito Matawalle ya yabawa jami’an rundunar soji da sauran hukumomin tsaro bisa sadaukarwar da suke yi wajen kare ƙasar nan, yana mai cewa wasu daga cikinsu sun rasa rayukansu yayin gudanar da aikin ƙasa.
Ya bayyana cewa dabarun tsaro da gwamnatin Tinubu ta ɗauka sun taimaka wajen kashe wasu fitattun shugabannin ‘yan bindiga tare da rusa maboyarsu, lamarin da ya kawo sauƙin matsalolin tsaro a yankuna da dama.
Ministan ya ƙara da cewa ingantuwar tsaro ta bai wa manoma da mazauna wasu yankuna damar komawa gonaki da sauran harkokin tattalin arziki.
Haka kuma ya ce ana samun ci gaba a yaƙi da ta’addanci a Arewa maso Gabas da kuma ƙoƙarin dakile rikice-rikicen ƙabilanci da ayyukan ta’addanci a wasu sassan Arewa ta Tsakiya.
Dangane da tattalin arziki, Matawalle ya ce shirin Renewed Hope Agenda na gwamnatin Tinubu na fara haifar da sakamako mai kyau a fannoni kamar tsaro, ababen more rayuwa, noma, tallafin jin ƙai da sauye-sauyen tattalin arziki.
Ya ce gwamnatin tarayya ta aiwatar da ayyuka da dama da suka amfani yankin Arewa, ciki har da gyaran hanyoyi, tallafin noma, samar da abinci, gina layukan dogo da bunƙasa harkokin makamashi.
Matawalle ya nuna kwarin gwiwa cewa nasarorin da gwamnatin Tinubu ke samu za su ƙara ƙarfafa goyon bayan al’umma kafin zaɓen shekarar 2027.
A ƙarshe, ya yi kira ga ‘yan siyasa da su fifita muradun ƙasa fiye da siyasa, tare da mara wa ƙoƙarin samar da zaman lafiya, tsaro da ci gaba baya a faɗin Najeriya.
