Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa an buɗe mashigar ruwa ta ‘Strait of Hormuz’ ga dukkan jiragen kasuwanci, bisa la’akari da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a Lebanon.
Ministan ya ce wannan mataki na cikin bin tsarin yarjejeniyar tsagaita wutar, domin tabbatar da cewa zirga-zirgar jiragen kasuwanci ba ta fuskanci tangarda a lokacin da yarjejeniyar ke aiki ba.
Wannan na nufin dukkan jiragen ruwa na kasuwanci za su ci gaba da wucewa ta mashigin ba tare da tsaiko ba, muddin suna bin dokokin tafiyar ruwa da aka tsara, kamar yadda kafar yada labarai ta Aljazeera ta Ruwaito.
Mashigin Strait of Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar mai da iskar gas a duniya, wanda ke da matuƙar tasiri ga kasuwannin makamashi na ƙasa da ƙasa.
A ‘yan makonnin da suka gabata, yankin ya fuskanci ƙarin tsauraran matakai saboda rikice-rikicen yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ya jawo damuwa kan zirga-zirgar jiragen ruwa.
Sai dai wannan sabuwar sanarwa ta Iran na nuna sassauta matsin lamba na wucin gadi, wanda ke da alaƙa kai tsaye da yarjejeniyar tsagaita wutar ba wai sauyi na dindindin ba.
