DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeKetareJihohin Amurka 25 sun kai ƙarar gwamnatin Trump kan kakaba haraji

Jihohin Amurka 25 sun kai ƙarar gwamnatin Trump kan kakaba haraji

Haɗakar jihohi 25 na Amurka, mafi yawansu na ƙarƙashin jagorancin gwamnonin jam’iyyar Democrat, sun shigar da ƙara gaban kotu domin ƙalubalantar sabon tsarin harajin shigo da kayayyaki na Shugaba Donald Trump.

A cewar su, Trump ya wuce ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen kakaba haraji kan kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashe da dama, kamar yadda gidan talabijin na TVC ya ruwaito.

An shigar da ƙarar ne a ranar Litinin a kotun kasuwancin ƙasa da ƙasa ta Amurka da ke New York. Jihohin suna neman kotun ta dakatar da aiwatar da harajin, ta ayyana shi a matsayin haramtacce, sannan ta umarci gwamnatin ta mayar da kuɗaɗen harajin da ta riga ta karɓa.

A cikin takardun da suka gabatar wa kotu, jihohin sun yi nuni da cewa ofishin wakilin kasuwanci na Amurka (USTR) ya yi amfani da batun aikin tilas a matsayin hujjar kakaba harajin, amma hakan bai dace da irin faɗin matakin da aka ɗauka ba.

Ƙarar ta shafi sabon tsarin harajin da Trump ya ƙaddamar a watan da ya gabata, inda ya sanya harajin tsakanin kashi 10 zuwa 12.5 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashe 60 da Amurka ke hulɗar kasuwanci da su.

An kakaba waɗannan haraje-harajen ne bayan binciken da ofishin USTR ya gudanar bisa zargin amfani da aikin tilas wajen samar da wasu kayayyaki, ƙarƙashin sashe na 301 na dokar kasuwanci ta shekarar 1974.

Tun bayan komawarsa mulki karo na biyu, Trump ya sauya salon kasuwancin Amurka da duniya ta hanyar kakaba haraji mai yawa kan ƙawayen Amurka da kuma sauran ƙasashe. Ya ce ƙasashen da Amurka ke kasuwanci da su sun daɗe suna cin moriyar tattalin arzikinta, kuma yana amfani da haraji a matsayin hanyar matsin lamba domin cimma sabbin yarjejeniyoyin kasuwanci.

Sai dai a ranar Litinin, Fadar White House ta mayar da martani kan ƙarar, inda ta ce matakin gwamnatin Trump na kakaba waɗannan haraje-harajen ya yi daidai da doka kuma yana cikin ikon gwamnati.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata