DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeSiyasaKotu ta fara karɓar shaida a shari'ar zargin El-Rufa'i da yin kutse...

Kotu ta fara karɓar shaida a shari’ar zargin El-Rufa’i da yin kutse a wayar NSA Ribadu

Kotu ta fara karɓar shaida a shari’ar zargin El-Rufa’i da yin kutse a wayar Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara

Kotun Tarayya da ke Abuja ta sake kunna bidiyon wata hira da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi, yayin da lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Deji Adeyanju, ya bayar da shaida a shari’ar zargin saurarar wayoyin tarho da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS) ta shigar a kan tsohon gwamnan.

Adeyanju ya bayyana a matsayin shaida ta biyu ga masu ƙara a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, inda ya shaida wa kotu cewa bidiyon hirar ya nuna daidai abin da ya gani a shirin Arise Television na ranar 13 ga Fabrairu, lokacin da El-Rufai ya yi ikirarin cewa an yi kutse tare da sauraron wata tattaunawar wayar tarho da ta shafi Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu.

A cikin shaidarsa, Adeyanju ya ce a ranar 12 ga Fabrairu rahotanni sun bayyana cewa ana shirin kama El-Rufai ko kuma gayyatarsa domin amsa tambayoyi daga hukumomin tsaro bayan dawowarsa daga birnin Cairo na ƙasar Egypt.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata