DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, April 20, 2026
HomeWasanniPSG za ta lashe gasar ‘Champions League’ karo na biyu - Carlo...

PSG za ta lashe gasar ‘Champions League’ karo na biyu – Carlo Ancelotti

Mai horas da tawagar kasar Brazil, kuma tsohon kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain na da babbar damar lashe kofin zakarun nahiyar Turai ‘UEFA Champions League’ a wannan kakar, wanda zai zama na biyu a tarihinsu idan hakan ta tabbata.

Wannan hasashe na Ancelotti ya jawo muhawara, musamman ganin yadda PSG ke ƙoƙarin kafa cikakkiyar ƙungiya mai ƙarfi da tasiri a nahiyar Turai tsawon shekaru, kamar yadda Fabrizio Romano ya wallafa.

Idan PSG ta cimma wannan buri, zai zama babban tarihi ga ƙungiyar, tare da ƙara tabbatar da matsayinta a cikin manyan kulob ɗin Turai.

Sai dai kuma masana da magoya bayan kwallon kafa na nuni da cewa akwai babban kalubale a gabanta kafin cimma wannan nasara, kasancewar akwai ƙungiyoyi masu ƙarfi da ke fafatawa a gasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata