DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, April 20, 2026
HomeLabaraiBabban hafsan tsaron Nijeriya Oluyede ya kai ziyarar aiki jihar Zamfara

Babban hafsan tsaron Nijeriya Oluyede ya kai ziyarar aiki jihar Zamfara

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Olufemi Oluyede, ya kai ziyara jihar Zamfara domin ganawa da sojoji da kuma shugabannin jihar kan halin tsaro da ake fuskanta a yankin.

Rahotanni sun nuna cewa Oluyede ya isa birnin Gusau, inda ya kai ziyara hedikwatar rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, wato Operation Fansan Yamma, a ziyararsa ta farko da ya kai jihar tun bayan hawansa wannan muƙami.

Babban hafsan tsaron ya samu tarba daga manyan hafsoshin soja, ciki har da kwamandan rundunar yankin, inda aka gabatar masa da cikakken bayani kan yadda ake gudanar da ayyukan yaƙi da ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro a yankin.

Bayan haka, ana sa ran zai gana da jami’an soji domin ƙarfafa musu gwiwa, tare da duba yadda ake gudanar da ayyukan tsaro kai tsaye a wasu wurare, kamar yadda gidan Talabijin na TVC ya ruwaito.

Haka kuma, ana shirin ya tattauna da Gwamna Dauda Lawal kan hanyoyin da za a ƙara inganta tsaro a jihar.

Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da jihar Zamfara ke ci gaba da fuskantar matsalolin hare-haren ‘yan bindiga, satar mutane da kuma rikice-rikicen tsaro, wanda ya jawo damuwa ga mazauna yankin da kuma hukumomi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata