Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da Sanata David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar ADC, tare da yin watsi da ƙarar da ɗan Majalisar Wakilai, Leke Abejide, ya shigar yana ƙalubalantar shugabancin jam’iyyar.
Mai shari’a Musa Liman ya ce kotun ba ta da hurumin tsoma baki cikin harkokin cikin gida na jam’iyya, sannan ya bayyana cewa ƙarar ba ta da tushe a doka.
Kotun ta kuma ce Abejide bai nuna cewa an tauye masa wani haƙƙi ba, kuma bai bi hanyoyin sasanta rikici na cikin jam’iyyar kafin ya garzaya kotu ba.
Mai shari’ar ya yanke hukuncin cewa miƙa shugabancin jam’iyyar daga Ralph Nwosu zuwa David Mark bai saɓa wa kundin tsarin mulkin ADC ba.
Kotun ta kuma amince cewa taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar 2 ga Yulin 2025 ya share fagen taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) da aka gudanar ranar 29 ga Yuli, wanda INEC ta sanya ido a kansa.
Saboda haka, kotun ta tabbatar da cewa zaɓen David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar da Rauf Aregbesola a matsayin sakatare ya yi daidai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar da Dokar Zaɓe ta 2026.
Kotun ta kuma umarci Abejide ya biya kowane ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙara diyyar naira miliyan biyu, yayin da lauyansa zai biya tarar naira miliyan 10 saboda karya tanadin Dokar Zaɓe ta 2026.
