DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeSiyasaKotun Tarayya ta soki matakin kashe makudan kuɗaɗe a sayen motocin majalisa

Kotun Tarayya ta soki matakin kashe makudan kuɗaɗe a sayen motocin majalisa

Kotu ta ayyana kashe biliyan N110bn kan motocin ‘yan majalisa da alawus a matsayin saɓa doka

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta ayyana kashe Naira biliyan 110 da Majalisar Tarayya ta yi kan sayen motoci da alawus-alawus ga mambobinta a matsayin abin da ya saɓa wa doka.

A hukuncin da Mai Shari’a Yellim Bogoro ya yanke, kotun ta ce kashe Naira biliyan 40 wajen sayen motoci 465 ga ‘yan majalisa da kuma Naira biliyan 70 a matsayin tallafin alawus ga sabbin mambobi ya saɓa wa dokokin saye da sayarwa na gwamnati da kuma amana da aka ɗora wa hukumomin gwamnati.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ƙungiyar SERAP ce ta shigar da ƙarar kan lamarin, inda kotun ta yi hukuncin cewa ya kamata a riƙa kashe kuɗaɗen jama’a bisa gaskiya da bin ƙa’idojin da suka dace.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata