DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, April 14, 2026
HomeSiyasaKotun ƙolin Nijeriya ta sanya 22 ga Afrilu domin sauraron ƙarar rikicin...

Kotun ƙolin Nijeriya ta sanya 22 ga Afrilu domin sauraron ƙarar rikicin PDP

Kotun Ƙolin Nijeriya ta sanya ranar 22 ga Afrilu domin sauraron shari’ar da aka ɗaukaka a gabanta da ta shafi rikicin shugabanci a jam’iyyar PDP.

Kararrakin sun fito ne daga tsagin shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki, wanda ke ƙalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a ranar 9 ga watan Maris.

Kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mohammed Garba ne ya tsayar da ranar, tare da amincewa da buƙatar gaggauta sauraron ƙarar, inda ya rage wa ɓangarorin lokacin gabatar da hujjoji.

Wannan shari’a ta samo asali ne daga hukuncin kotu da ya hana jam’iyyar gudanar da babban taronta na kasa har sai ta bi dokokin da suka shafi zabe da tsarin cikin gida.

A zaman kotun, manyan ƴan siyasa sun halarta ciki har da gwamnan Oyo, Seyi Makinde, tare da Turaki da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.

Ana sa ran hukuncin kotun koli zai zama mataki na ƙarshe wajen warware rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar kafin zaɓukan gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata