Tsohon Gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban Nijeriya na jam’iyyar NDC , Rabi’u Musa Kwankwaso, ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa yana shirin gudanar da zanga-zanga kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Kwankwaso ya ce saƙon da ake yaɗawa ba gaske ba ne kuma ba ya wakiltar matsayarsa ko ta jam’iyyarsa, tare da gargadin jama’a da su guji yaɗa abin da ya bayyana a matsayin bayanan ƙarya.
Kwankwaso ya jaddada cewa shi da jam’iyyarsa ba sa goyon bayan duk wani mataki da zai iya tada zaune tsaye ko lalata rayuka da dukiyoyi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Ya ƙara da cewa jam’iyyarsu na ci gaba da kasancewa mai biyayya ga hanyoyin zaman lafiya da bin doka wajen magance ƙalubalen ƙasa, yana mai cewa tsarin dimokuraɗiyya ne kaɗai halastacciyar hanyar samar da sauyin siyasa.
Kwankwaso ya kuma bayyana cewa ya kamata a warware korafe-korafen siyasa ta hanyar akwatin zaɓe maimakon zanga-zanga, yana mai nuna kwarin gwiwa kan damar jam’iyyarsa a zaɓe mai zuwa.
