Ɗan takarar mataimakin shugaban Nijeriya na jam’iyyar APM, Lawal Daura, ya ce ba za su amince da duk wani yunƙurin yin magudi domin karkatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba, yana mai cewa masu shirin yin hakan “za su sha mamaki”.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Daura ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓe na kasa na Makinde-Daura Presidential Campaign Organisation.
Tsohon Darakta-Janar na hukumar tsaro ta (DSS) ya ce duk wani yunƙurin murɗe zaɓen 2027 za su yi adawa da shi, yana mai jaddada cewa ya kamata a gudanar da zaɓen bisa tanadin doka da dokar zaɓe.
Daura ya ce jam’iyyun siyasa da ’yan takara ya kamata su nemi goyon bayan ’yan Nijeriya ta hanyar gabatar da manufofi masu gamsarwa da kuma ’yan takarar da suka dace, maimakon neman wasu hanyoyin da ba su dace ba.
Ya bayyana cewa adadin masu rajista da ke da damar kaɗa ƙuri’a a Nijeriya ya haura miliyan 100, lamarin da ya ce yana nuna girman yawan masu zaɓe da kuma muhimmancin zaɓen 2027.
A cewarsa, ’yan siyasar da ke fafutukar neman mulki na buƙatar yin aiki tukuru wajen jan hankalin mafi yawan masu kaɗa ƙuri’a, yana mai cewa tawagar APM na da burin samun goyon bayan wani kaso mai yawa na masu zaɓe.
Daura ya ce wannan karon za su mayar da hankali wajen tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen bisa ƙa’ida, tare da bin tanadin dokar zaɓe da sauran dokokin da suka shafi gudanar da zaɓe.
Ya kuma yi gargadin cewa duk masu tunanin za su iya amfani da magudi ko wata hanya ta daban wajen samun nasara a zaɓen, a cewarsa, za su gamu da adawa.
Daura ya bayyana manufar APM da cewa ita ce “sake fasalin Nijeriya”, yana mai cewa cimma wannan buri na buƙatar mutane masu inganci, jajircewa, mayar da hankali da kuma ƙudurin kawo sauyi.
A nasa ɓangaren, Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen, Felix Hayat, ya ce tawagar da aka kafa ta ƙunshi mutane da suke da niyyar tunkarar matsalolin da ƙasar ke fuskanta.
Hayat ya yi kira ga matasan Nijeriya da kada su yanke shawarar siyasa bisa addini, ƙabila ko ra’ayin yankin da suka fito kawai.
Ya ce matasa na da makomar ƙasar a hannunsu, don haka ya kamata su yi tunani mai zurfi kafin yanke shawara, tare da fahimtar irin tasirin zaɓensu ga makomarsu.
Shi ma shugaban jam’iyyar APM na ƙasa, Yusuf Dantalle, ya buƙaci mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen da aka ƙaddamar da su yi aiki tare da tsarin jam’iyyar domin cimma manufofinta.
Dantalle ya ce manufarsu ita ce ganin Seyi Makinde da Lawal Daura sun samu nasarar lashe zaɓen 2027 tare da kafa gwamnati a ƙarƙashin APM.
Ya kuma amince cewa rashin jituwa na iya tasowa a cikin kowace ƙungiyar siyasa, amma ya ce yadda mambobin ƙungiyar za su magance bambance-bambancen ra’ayi ne zai taimaka wajen ƙarfafa ko raunana ayyukansu.
Shugaban jam’iyyar ya kuma buƙaci sabbin mambobin kwamitin da aka rantsar da su ɗauki nadin da aka yi musu a matsayin farkon aikin, ba wai nasara ko ƙarshen tafiya ba.
