Shugaban ƙasar Saliyo, Julius Maada Bio, ya ce ba za a iya samun dorewar zaman lafiya a duniya ba tare da jagorancin Afirka ba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Bio ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi ga shugabannin duniya a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, da ke gudana a birnin New York.
Ya koka kan rashin wakilcin Afirka na dindindin a kwamatin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, yana mai cewa tsarin majalisar har yanzu yana kama da tsarin duniya na shekarar 1945.
Shugaban ya ce Afirka, wadda ke da sama da mutane biliyan 1.6, ba ta da kujerar dindindin a kwamatin tsaron, duk da irin muhimmancin batutuwan nahiyar da majalisar ke tattaunawa a kai.
A cewarsa, kwamatin tsaro ba zai samu cikakken halacci da tasiri ba matuƙar aka ci gaba da barin wata nahiya gaba ɗaya daga matakin yanke manyan shawarwarin duniya.
Bio ya ce Afirka na buƙatar kujeru biyu na dindindin da kuma kujeru biyar marasa dindindin a kwamatin tsaron, yana mai cewa Saliyo za ta ci gaba da jagorantar wannan buƙata a matsayin mai kula da kwamitin ƙasashe 10 na tarayyar Afirka.
Ya ƙara da cewa babu wata mafita mai ɗorewa kan zaman lafiya, sauyin yanayi, abinci, makamashi da fasaha da za a iya samarwa ba tare da cikakkiyar gudummawar da jagorancin Afirka ba.
