Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya yi magana kan yadda wasu abokansa, ’yan siyasa da ’yan uwansa suka yi shiru a lokacin da yake fuskantar ƙalubale.
Jaridar Premium Times ta ruwaito El-Rufa’i, wanda ke hannun hukumar ICPC kan zarge-zargen almundahana, ya wallafa wata sanarwa a Facebook mai taken “My Relationships and the Aftermath”.
Ya ce a tsawon rayuwarsa ya riƙa tsayawa tare da mutane da kuma wasu manufofi da ya yi imanin cewa sun dace, ba tare da neman yabo ko sakayya ba.
A cewarsa, imaninsa na Musulunci, tarbiyyarsa ta Arewa da kuma lamirinsa ne suka jagoranci irin waɗannan halaye da ya ɗauka a baya.
El-Rufai ya ce mutanen da ya taɓa tallafa wa suna da ’yancin yin nasu zaɓin a yanzu da yanayi ya sauya, ko su yi magana ko kuma su yi shiru.
Ya ƙara da cewa ƙalubale kan bayyana ainihin yanayin wasu alaƙa, amma ya ce ba ya da nadamar tsayawa tare da mutanen da ya yi imanin ya dace ya taimaka musu.
Tsohon gwamnan ya ce ba ya neman ramuwar gayya kan duk wani rashin adalci ko cutarwa da aka yi masa, yana mai cewa ya bar hukuncin komai ga Allah, domin abin da ya fi damunsa shi ne ya kasance cikin kwanciyar hankali da lamirinsa.
