DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiNdume ya buƙaci a kubutar da mutanen Borno, bayan ceto ɗaliban Oyo

Ndume ya buƙaci a kubutar da mutanen Borno, bayan ceto ɗaliban Oyo

Sanatan da ke wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya yi kira ga jami’an tsaro su ƙara kaimi wajen ceto mutanen da har yanzu suke hannun masu garkuwa da su a mazaɓarsa, bayan nasarar kuɓutar da ɗalibai da malamai da aka sace a Jihar Oyo.

Jaridar Punch ta ruwaito Ndume ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.

A yayin hirar, Ndume ya buƙaci rundunar sojin Najeriya ta karkata hankalinta zuwa Borno ta Kudu domin ceto mutanen da ke ci gaba da kasancewa a tsare.

Kiran nasa ya biyo bayan kuɓutar da ɗalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a Jihar Oyo, bayan shafe fiye da kwanaki 50 suna hannun masu garkuwa da mutane.

Da yake magana da kan nasarar aikin ceton, Ndume ya ce lokaci ya yi da jami’an tsaro za su mayar da hankali kan halin da mutanen Borno ta Kudu ke ciki.

“Ina amfani da wannan dama wajen roƙon rundunar soji da ta karkata hankalinta zuwa mazaɓata domin a ceto mutanenmu.

Har yanzu mutane 42, ciki har da yara, na ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa da su,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa an yi garkuwa da fiye da mutum 30 daga garin Lassa a kwanan nan, yayin da sama da mutum 50 ke ci gaba da zama a tsare a wani wuri na daban.

A cewarsa, duk da cewa an sako wasu daga cikin fiye da mutum 400 da aka yi garkuwa da su a baya, har yanzu jama’a da dama na ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa da mutane.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata