Nijeriya da Amurka sun rattaba sabuwar yarjejeniyar da za ta ƙarfafa zuba jarin Amurka a fannin ma’adinai na Nijeriya.
DWAfrirka ta ruwaito an rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya na UNGA da ke gudana a birnin New York, tsakanin ministan ma’adinai na Nijeriya, Dele Alake, da mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka, Christopher Landau.
Yarjejeniyar na da nufin jawo ƙarin jarin ƙasashen waje zuwa fannin ma’adinai na Nijeriya, wanda ake kiyasta cewa darajarsa ta kai kusan dala biliyan 700.
Nijeriya na da dimbin arzikin ma’adinai da suka haɗa da lithium, zinariya, tin, duwatsu masu daraja, ƙarafa da phosphate.
Jami’an Nijeriya sun bayyana cewa manufar yarjejeniyar ba wai fitar da ɗanyen ma’adinai kaɗai ba ce, illa samar da masana’antun sarrafa ma’adinai a cikin ƙasar.
Sun ce hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, bunƙasa ƙwarewar ma’aikata da kuma tabbatar da cewa Nijeriya ta riƙe kaso mai yawa na ribar tattalin arzikin da ake samu daga albarkatun ƙasar.
Haka kuma, yarjejeniyar na iya ƙara wa Nijeriya muhimmanci a gasar duniya ta neman ma’adinan da ake buƙata sosai, musamman lithium, wanda ke da muhimmiyar rawa wajen kera batir ɗin motocin lantarki da fasahohin makamashi na zamani.
