DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeLabaraiKotu ta hana Akanta Janar na Bauchi zuwa aikin Hajji da duba...

Kotu ta hana Akanta Janar na Bauchi zuwa aikin Hajji da duba lafiya a Saudiyya

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar da Akanta Janar na jihar Bauchi, Sirajo Muhammad Jaja ya gabatar domin samun izinin zuwa kasar Saudiyya aikin Hajji da kuma duba lafiyarsa.

Mai shari’a O.A. Egwuatu ne ya yanke hukuncin, bayan lauyoyin masu gabatar da kara sun bayyana wa kotun cewa wanda ake tuhumar na iya tserewa, musamman ganin cewa wasu da ake zargi tare da shi har yanzu ba a kama su ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Hukumar EFCC na tuhumar Sirajo Jaja tare da Aliyu Abubakar, wani mai sana’ar canjin kuɗi, bisa sabuwar takardar tuhuma mai ƙunshe da tuhume-tuhume guda biyar.

A cewar takardar karar, ana zargin su da karkatar da kuɗaɗen gwamnatin jihar Bauchi da kuma halasta kuɗaɗen haram da suka kai Naira biliyan 1.6.

A zaman kotun na ranar Talata, lauyan Sirajo Jaja, Chris Uche SAN, ya roki kotun ta ba wanda yake karewa izinin tafiya Saudiyya na tsawon makonni biyu domin gudanar da aikin Hajji da kuma duba lafiyarsa.

Sai dai lauyan masu gabatar da kara, Abba Muhammed SAN, ya shaida wa kotun cewa sun karɓi bukatar tare da gabatar da martani na adawa da ita, inda suka nace cewa wanda ake kara na iya guduwa idan aka ba shi damar fita kasar.

Ya bayyana cewa masu gabatar da karar sun gabatar da hujjoji cikin kundin rantsuwa mai sakin layi goma tun ranar 13 ga Maris, 2026 domin nuna dalilin kin amincewa da bukatar.

Bayan sauraron bangarorin biyu, Mai shari’a Egwuatu ya yi watsi da bukatar tare da dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 30 ga Yuni, 2026.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata