Majalisar dokokin ƙasar Senegal ta zaɓi tsohon firaminista, Ousmane Sonko, a matsayin kakakin majalisar dokokin ƙasar bayan dawo da shi majalisar a zaman da ‘yan adawa suka kaurace wa halarta.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Sonko, wanda shi kaɗai ne ya tsaya neman takarar, ya samu ƙuri’u 132 yayin da babu wani ɗan majalisa da ya kaɗa ƙuri’ar adawa da shi, sai mutum guda da ya kaurace wa jefa ƙuri’a.
Jami’in da ya jagoranci zaman majalisar, Ismael Diallo, ya bayyana cewa majalisar dokokin Senegal na da kujeru 165 gaba ɗaya.
Zaɓen Sonko na zuwa ne bayan sauye-sauyen siyasa da suka faru a ƙasar, inda ya rasa mukamin firaminista kafin daga baya aka dawo da shi cikin majalisar dokoki.
