Jigo a jam’iyyar PDP, Dan Ulasi, ya yi gargadin cewa jam’iyyar ba za ta iya kayar da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a zaɓen 2027 ba muddin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, na matsayin jagoranta na ƙasa.
Ulasi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Arise TV ranar Alhamis, inda ya ce akwai rikice-rikice a cikin jam’iyyar da ke hana ta yin tasiri.
DCL Hausa ta ruwaito cewa Ulasi ya ce ba zai ci gaba da zama a jam’iyyar ba idan ba a warware wannan sabani ba, yana mai cewa ba zai yi aiki a cikin tsarin da ke cike da rikitarwa ba.
Ya ce ba zai yiwu Wike ya kasance jagoran PDP a lokaci guda yana goyon bayan Shugaba Tinubu ba, yana mai cewa hakan na iya kawo cikas ga jam’iyyar a zaɓe mai zuwa.
Ulasi ya kuma bayyana cewa ya gana da Peter Obi sau da dama, yana yaba masa kan hangen nesansa, duk da cewa bai bayyana wata sabuwar alaka ta siyasa ba.
