Jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ta bayyana cewa an miƙa sunan tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ga hukumar zaɓen Nijeriya INEC a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa domin zaɓen shekarar 2027, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
Sakataren yaɗa labarai na tsagin, Ini Ememobong, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja, inda ya ce sun kuma miƙa sunayen ‘yan takarar gwamnoni da na Majalisar Dokoki ta Kasa.
Ya ce an miƙa sunayen ne da hannu, saboda tsagin bai samu damar amfani da shafin intanet na INEC wajen lodawa ba, yana mai cewa hakan ya yi daidai da tanade-tanaden dokar zaɓe ta 2026.
Ememobong ya ce sun karɓi takardar tabbatar da karɓar jerin sunayen daga INEC, duk da cewa hukumar ba ta ba su lambar shiga shafinta ba.
Ya buƙaci magoya bayan tsagin kada su karaya idan har INEC ba ta wallafa sunayen ‘yan takararsu ba, yana mai cewa suna amfani da duk hanyoyin doka da kundin tsarin mulki domin kare abin da suka kira sahihancin jam’iyyar PDP.
Har ila yau, ya zargi INEC da nuna son kai a rikicin cikin gida na jam’iyyar, yana mai cewa jami’an hukumar sun ɓoye wasu muhimman bayanai a kotu duk da cewa sun halarci taruka da zaɓukan cikin gida na PDP.
Ememobong ya kuma bayyana cewa tsagin ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun ɗaukaka kara bayan hukuncin babbar kotun tarayya da ke Abuja, wanda Alƙali Salim Ibrahim ya yanke, yana mai cewa hukuncin ya saɓa da wasu hukunce-hukuncen kotun koli da kotun ɗaukaka kara.
Ya ƙara da cewa kwafin hukuncin da kotu ta ba su bai yi daidai da abin da alƙalin ya karanta a zaman kotu ba, lamarin da ya ce ya sa suka nemi kotun ɗaukaka ƙara ta fayyace batun.
Tsagin ya jaddada cewa zai ci gaba da fafutukar kare tsarin jam’iyyu masu yawa a Nijeriya ta hanyar bin doka, yana mai bayyana cewa suna da yaƙinin samun nasara a ƙarshe.
