Hauhawar farashi a Birtaniya ta karu zuwa kashi 3.3 cikin 100 a watan Maris na shekarar 2026, sakamakon tashin farashin mai da iskar gas da rikicin Gabas ta Tsakiya ya haifar.
Hukumar kididdiga ta kasar Burtaniya-ONS, ta ce ta bayyana hakan, inda ta ce hauhawar ya laru daga kashi 3.0 cikin 100 da aka samu a watan Fabrairu.
Masanin tattalin arziki na hukumar, Grant Fitzner, ya ce karin ya samo asali ne daga tashin farashin makamashi, musamman man fetur, wanda ya yi tashin gwauron zabi cikin sama da shekaru uku.
Ministar kudi ta kasar, Rachel Reeves, ta ce rikicin ba nasu bane, amma yana kara tsadar rayuwa ga jama’a da kamfanoni.
Ta kara da cewa gwamnati na kokarin rage radadin wannan tsadar, ciki har da karin haraji kan masu samar da wutar lantarki da ke da karancin gurbata muhalli.
Rikicin da ke gudana tsakanin Amurka da Iran ya janyo tashin farashin makamashi tun daga karshen watan Fabrairu, lamarin da ya kara dagula tattalin arziki a kasashen duniya.
