Jam’iyyar PDP da ke ƙarƙashin jagorancin Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya sanya kuɗin fom ɗin neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 zuwa Naira miliyan 51.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an cimma wannan matsaya ne a taron kwamitin zartarwar jam’iyyar na kasa NEC, na bangaren jam’iyyar da aka gudanar a Abuja, inda aka amince da cewa fom ɗin nuna sha’awa zai kasance Naira miliyan 1, yayin da fom ɗin tsayawa takara zai kai Naira miliyan 50.
Jam’iyyar PDP na cikin rikicin shugabanci tun shekarar da ta gabata, wanda ya haifar da ɓangarori biyu, ɗaya karkashin Abdulrahman Mohammed da ke samun goyon bayan Wike, yayin da ɗayan ke ƙarƙashin Kabiru Tanimu Turaki wanda gwamnoni ke mara masa baya.
Majiyar jam’iyyar ta ce an riga an fara shirye-shiryen zaɓen fidda gwani.
Duk da cewa Nyesom Wike ya nuna goyon bayansa ga shugaba Bola Ahmed Tinubu, bangaren jam’iyyar ya jaddada cewa zai fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
