Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da ɗaukar matakai domin tabbatar da dawowar ɗaliban makaranta da sauran mutanen da aka sace cikin ƙoshin lafiya.
Shettima ya bayyana hakan ne a Abuja bayan kammala sallar Juma’a da aka gudanar a babban Masallacin Abuja domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta bana.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito Shettima ya ce gwamnatin Tinubu ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a faɗin ƙasar nan.
Ya tabbatar da cewa gwamnati na aiki ba dare ba rana domin ceto waɗanda aka sace da kuma magance matsalar rashin tsaro.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa ƙasa addu’ar zaman lafiya da haɗin kai.
Mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada cewa duk da ƙalubalen da ake fuskanta, gwamnati na da ƙudirin dawo da kwanciyar hankali a Najeriya.
Wannan bayani na Shettima ya zo ne bayan Shugaba Tinubu ya amince da ɗaukar sabbin masu tsaron daji 1,000 domin ƙarfafa tsaro, musamman bayan sace ɗalibai da malamai da aka yi a Ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo.
Shettima ya buƙaci ‘yan ƙasa su kasance masu haƙuri tare da ci gaba da addu’a ga Najeriya da shugabanninta, yana mai cewa abubuwan da ke haɗa kan ‘yan Najeriya sun fi waɗanda ke rarraba su yawa.
Daga nan ya kuma yabawa waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu da ƙoƙarinsu wajen tabbatar da dimokuraɗiyyar da Najeriya ke mora a yau, yana mai cewa ya kamata a ci gaba da tunawa da gudummawar da suka bayar wajen gina ƙasa.
