Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan matakan da yake ɗauka wajen yaƙi da ta’addanci da rashin tsaro a Nijeriya, musamman hare-haren da ake kai wa al’ummomin Kiristoci.
Trump ya bayyana hakan ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 6 ga Yuli, 2026, wadda mai ba Tinubu shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba.
A cikin wasiƙar, Trump ya ce yana yaba wa Tinubu bisa jajircewarsa wajen magance matsalolin da ke addabar Nijeriya, musamman tashe-tashen hankulan da suka shafi al’ummomin Kiristoci.
Ya kuma jaddada cewa Amurka da Nijeriya suna da manufa ɗaya ta yaƙi da ta’addanci ta kowace siga, yana mai cewa ƙasashen biyu sun samar da tsarin haɗin gwiwar tsaro na shekarar 2026 domin ƙarfafa wannan yaƙi.
Trump ya ce Amurka ta tura jami’an rundunar ta musamman da ake kira Special Operations Forces domin tallafa wa sojojin Nijeriya da horo, kayan aiki da bayanan sirri da za su taimaka wajen kare ƙasar da tabbatar da tsaron al’ummarta.
A cewar fadar shugaban kasa, Nijeriya da Amurka sun ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro a cikin ‘yan watannin nan, musamman ta hanyar kafa wata ƙungiyar haɗin gwiwa da masu ba shugabannin ƙasashen biyu shawara kan harkokin tsaro ke jagoranta.
Haɗin gwiwar ya mayar da hankali kan horar da jami’an tsaro, musayar bayanan sirri da gudanar da ayyukan haɗin gwiwa kan ƙungiyoyin ta’addanci.
Fadar shugaban ƙasar ta kuma ce ɗaya daga cikin sakamakon wannan haɗin gwiwa shi ne wani samame na haɗin gwiwa da aka gudanar a ranar 16 ga Mayu kan maboyar ISIS a yankin tafkin Chadi, wanda rahotanni suka ce ya yi sanadin hallaka shugaban ƙungiyar, Abubakar Al-Minoki, tare da wasu daga cikin kwamandojinsa.
