‘Yan sandan jihohi za su ƙarfafa tsarin tsaron al’ummar Nijeriya – IGP Disu
Sufeto Janar na Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, Tunji Disu, ya bayyana cewa kafa rundunar ‘yan sandan jihohi za ta ƙarfafa tsarin tsaron al’umma, inganta tattara bayanan sirri da kuma kusantar da ayyukan tsaro ga jama’a.
Jaridar Punch ta ruwaito Disu ya furta hakan ne yayin taron Shugabannin ‘yan sanda na Majalisar dinkin duniya uniya da aka gudanar a birnin New York.
Tunji Disu ya ce aiwatar da tsarin zai buƙaci cikakken nazari, tattaunawa da masu ruwa da tsaki, koyon darasi daga ƙasashen da ke amfani da irin wannan tsari da kuma gina ƙwarewar jami’an tsaro kafin fara aikin gaba ɗaya.
A cewarsa, rundunar ‘yan sandan jihohi za ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro na tarayya da na jihohi, tare da bai wa jami’an tsaro damar fahimtar al’ummomin da suke aiki a cikinsu, abin da zai ƙara yawan amincewar jama’a da inganta tattara bayanan sirri da saurin kai ɗauki lokacin da matsalar tsaro ta taso.
Disu ya kuma sake jaddada ƙudirin rundunar ‘yan sanda na ci gaba da rungumar sabbin dabaru, ƙwarewa da haɗin gwiwa domin tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban ƙasa.
Ya kuma yabawa rawar da Nijeriya ke takawa a ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya, yana mai cewa ƙasar ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi bayar da gudunmawa tun bayan fara irin waɗannan ayyuka a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a shekarar 1960.
