DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, October 6, 2026
HomeLabaraiMun kafa sabbin rundunonin soji domin yaƙi da barazanar tsaro - Tinubu

Mun kafa sabbin rundunonin soji domin yaƙi da barazanar tsaro – Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce rundunar sojin Nijeriya ta fara aiki da sabbin rundunonin soji a jihohin Zamfara, Kebbi, Oyo da Osun, a wani mataki da ya ce zai ƙara kusantar da jami’an tsaro da al’ummomin da ke fuskantar barazanar tsaro.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi ta wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya bayyana matakan da gwamnatin Nijeriya ke ɗauka domin ƙarfafa ƙarfin aiki da walwalar jami’an tsaron ƙasar.

Shugaban ya ce kafa sabbin rundunonin zai taimaka wajen kusantar da sojoji da al’ummomin da ke cikin haɗari, tare da ƙara musu damar mayar da martani cikin gaggawa idan wata barazana ta taso.

A cewarsa, sabbin rundunonin da aka fara aiki da su a Zamfara, Kebbi, Oyo da Osun wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙara ƙarfin rundunar sojin Nijeriya wajen tunkarar matsalolin tsaro.

Tinubu ya ce kasancewar sojoji kusa da al’ummomin da ke cikin haɗari zai taimaka wajen inganta saurin ɗaukar mataki idan rayukan jama’a ko dukiyoyinsu suka shiga cikin haɗari.

Kafin wannan sanarwar, rundunar sojin Nijeriya ta riga ta fara shirye-shiryen gudanar da ayyukan sabbin rundunonin a wasu daga cikin wuraren.

A ranar 1 ga Oktoba, babban kwamandan runduna ta biyu, Manjo Janar Auwalu Mahmuda, ya duba sabon hedikwatar Birged ta 7 a Oyo da bataliya ta 137 da ke Ile-Ife a jihar Osun.

Tinubu ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya na hanzarta gina sabbin barikoki da ma’ajiyar kayan soji a Abuja, Ekiti, Ebonyi da Kogi, yayin da ya ce an riga an kammala wani aikin a jihar Osun.

Ya ce ƙara wa jami’an tsaro nauyin aiki ya kamata ya kasance tare da ƙarin tallafi gare su da iyalansu, saboda iyalan jami’an tsaro ma suna fuskantar wasu nauyin da ke tattare da tura ’yan uwansu wuraren aiki.

Shugaban ya kuma bayyana cewa ƙarin albashin da aka yi wa jami’an rundunar sojin Nijeriya da sauran jami’an tsaron ƙasar na baya-bayan nan ya fara kawo sauyi a rayuwarsu da ta iyalansu.

Tinubu ya ce ya samu ra’ayoyin wasu jami’an tsaro kan yadda ƙarin albashin ya shafe su, yana mai cewa yana farin ciki da yadda suke bayyana cewa matakin yana kawo sauƙi a rayuwarsu.

Ya jaddada cewa tura jami’an tsaro zuwa wuraren da ake fuskantar barazanar tsaro ba ya shafar jami’an kaɗai, domin iyalansu ma suna taka rawa wajen ɗaukar nauyin da ke tattare da aikin.

Shugaban wanda shi ne babban kwamandan rundunar sojin Nijeriya, ya ce wajibi ne gwamnati ta tabbatar da cewa jami’an tsaro suna samun kayan aiki da tallafin da suke buƙata domin gudanar da ayyukansu.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da iyalansu yayin da suke gudanar da ayyukan kare ƙasa.

Kafa sabbin rundunonin ya zo ne a daidai lokacin da wasu sassan Nijeriya ke ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro, musamman hare-haren ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran barazanar da ke addabar wasu al’ummomi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata