DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, October 6, 2026
HomeLabaraiMajalisar dattawa ta ce ba za ta sake duba dokar zaɓe kafin...

Majalisar dattawa ta ce ba za ta sake duba dokar zaɓe kafin 2027 ba

Majalisar dattawan Nijeriya ta ce ba za ta sake duba ko yin wani sauyi a dokar zaɓe ta 2026 kafin gudanar da babban zaɓen shekarar 2027 ba, tana mai cewa an riga an kammala aikin gyaran dokar kuma yanzu ana amfani da ita wajen shirye-shiryen zaɓen.

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan yaɗa labarai da harkokin jama’a, Sanata Yemi Adaramodu, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da jaridar Punch ta yi da shi, yayin da yake magana kan hukuncin kotun koli da ya dawo da wasu tanade-tanaden dokar.

Adaramodu ya ce majalisar kasa ta kammala aikin gyaran dokar zaɓe ne domin a yi amfani da ita a babban zaɓen 2027, don haka ba zai dace a sake sauya dokar a lokacin da shirye-shiryen zaɓen suka yi nisa ba.

A cewarsa, duk wanda yake da ƙorafi ko buƙatar a yi wani sauyi a dokar zai iya gabatar da ƙorafinsa ga majalisar dattawa, amma matsayar majalisar ita ce dokar da aka amince da ita kuma shugaban kasa ya rattaba hannu a kanta za ta ci gaba da aiki.

Sanatan ya bayyana cewa tuni jam’iyyun siyasa suka fara amfani da tanade-tanaden dokar wajen gudanar da harkokin cikin gida da kuma samar da ’yan takarar da za su fafata a zaɓen 2027.

Kotun kolin, wadda ta kunshi alkalai bakwai, ta yanke hukuncin baki ɗaya cewa tanade-tanaden da ake takaddama a kansu ba sa saɓa wa kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Sassan 77(5), 77(6) da 77(7) na dokar sun shafi rajistar ’yan jam’iyyu da kuma wasu sharuddan da suka shafi shiga zaɓen fidda gwani, yayin da sashe na 84(2) ya tanadi hanyoyin da jam’iyyu za su bi wajen tsayar da ’yan takara, ciki har da zaɓen fidda gwani kai tsaye ko cimma matsaya ta hanyar yarjejeniya.

Duk da haka, hukuncin kotun kolin ya sake haifar da tambayoyi kan yadda waɗannan tanade-tanade za su iya shafar wasu ’yan takara, musamman batutuwan da suka shafi kasancewa mamba a jam’iyya, rangwame ko tsarin da aka bi wajen tsayar da su.

Sai dai wasu manyan jam’iyyun siyasa, ciki har da PDP, APM da Labour Party, sun bayyana cewa ’yan takararsu ba su cikin wani hali da zai sa a soke takararsu sakamakon hukuncin kotun koli.

Haka kuma, jam’iyyar NDC ta yi watsi da fargabar cewa hukuncin zai iya shafar takarar ɗan takarar shugaban ƙasarta, Peter Obi, da abokin takararsa Rabiu Kwankwaso, da kuma tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege.

Sakataren yaɗa labarai na kasa na NDC, Osa Director, ya ce bai kamata a riƙa fassara hukuncin kotun koli bisa ra’ayin mutum ɗaya ba, yana mai cewa duk wanda yake ƙalubalantar cancantar wani ɗan takara ya kamata ya kai ƙarar tasa gaban kotu.

Hukuncin kotun kolin ya samo asali ne daga takaddamar shari’a kan sahihancin wasu tanade-tanaden dokar zaɓe ta 2026, bayan da kotun daukaka kara ta bayyana wasu daga cikinsu a matsayin waɗanda suka saɓa wa kundin tsarin mulki.

Sai dai hukumar zaɓen Nijeriya, INEC, ta garzaya kotun koli, wadda daga bisani ta soke hukuncin kotun ɗaukaka kara tare da dawo da tanade-tanaden da ake takaddama a kansu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata