DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 9, 2026
HomeSiyasaZa mu tabbatar da haɗin kan 'yan Nijeriya duk da bambance-bambancen da...

Za mu tabbatar da haɗin kan ‘yan Nijeriya duk da bambance-bambancen da ke tsakaninsu – Tinubu

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya ce Gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar tabbatar da haɗin kan ƙasar, duk da bambance-bambancen addini, ƙabila da ra’ayi da ke tsakanin ’yan ƙasar.

Tinubu, wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya wakilta, ya bayyana hakan ne a ranar Talata a taron ƙasa kan tsaro da haɗin kan Nijeriya da ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), tare da haɗin gwiwar Muslim World League, suka shirya.

Shugaban ya ce tattaunawa da fahimtar juna na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba da kasancewar Nijeriya a matsayin ƙasa ɗaya.

Ya kuma ce Gwamnatin Nijeriya na ƙoƙarin magance matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar, tare da yin aiki da sauran ƙasashe wajen inganta zaman lafiya a duniya.

Tinubu ya bayyana taron a matsayin wanda ya zo a kan lokaci, ganin yadda duniya ke fuskantar matsalolin tsaro daban-daban, yana mai cewa shawarwarin da za a cimma za su taimaka wajen neman zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Afirka da duniya baki ɗaya.

A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya gargadi ’yan siyasa da kada su riƙa amfani da addini ko ƙabilanci domin cimma manufofin siyasa.

Yilwatda ya ce bambancin addini da ƙabila ya kamata ya zama abin ƙarfafa Nijeriya, ba hanyar raba ’yan ƙasar ba. Ya kuma bayyana cewa tashin hankali ba ya bambanta tsakanin Kirista da Musulmi, domin kowa na iya fuskantar illarsa.

Ya yi kira ga malaman addinai da su mayar da masallatai da majami’u cibiyoyin zaman lafiya, sulhu da wayar da kan jama’a, tare da yin wa’azi ba tare da ƙiyayya, cin mutunci ko tunzura jama’a ba.

Shi ma babban sakataren Nigeria Inter-Religious Council (NIREC), Farfesa Cornelius Omonokhua, ya bukaci Musulmi da Kiristoci su ƙarfafa tausayi, ƙauna da mutunta rayuwar ɗan Adam.

A nasa ɓangaren, Sarkin Musulmi kuma shugaban haɗin gwiwar NIREC, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce Nijeriya ba ta rasa hanyoyin magance matsalolinta, abin da ya fi bukata shi ne aiwatar da yarjejeniyoyin da ake cimmawa a taruka.

Sarkin ya kuma yi kira ga Musulmi da Kiristoci da su guji zagin juna, yana mai cewa mutunta juna da zaman lafiya su ne hanyoyin tabbatar da haɗin kan ƙasa.

Taron ya samu halartar babban sakataren Muslim World League, Sheikh Mohammad Al-Issa, wanda ya zo Nijeriya domin shaida rattaba hannu kan Yarjejeniyar Abuja, wadda ke da nufin ƙulla sabuwar haɗin gwiwa tsakanin shugabannin Musulmi da Kiristoci da kuma samar da tsarin gina zaman lafiya a Nijeriya da yammacin Afirka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata