Jam’iyyar APC a jihar Kano ta fitar da jerin sunayen mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna gabanin babban zaɓen 2027, inda ta haɗa fitattun malaman addinin Musulunci, ’yan siyasa da manyan jami’an gwamnati a jihar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Shugaban APC na jihar Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa, ne ya sanar da fitar da jerin sunayen kwamitin, kamar yadda mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne zai jagoranci kwamitin, yayin da mataimakinsa, Murtala Sule Garo, zai zama mataimakin shugaban kwamitin, a wani mataki na shirye-shiryen jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.
Daga cikin fitattun malaman addinin Musulunci da aka saka cikin kwamitin akwai tsohon shugaban hukumar jin daɗin Alhazai ta kasa (NAHCON), Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan, da kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Sauran malaman addinin da aka saka sun haɗa da Sheikh Ali Dan Abba, wanda shi ne babban kwamishina a hukumar Shari’a ta jihar Kano, da kuma fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Nazifi Bichi.
Haka kuma, jerin sunayen ya ƙunshi tsoffin gwamnonin Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da Malam Ibrahim Shekarau, tare da Sanata Kabiru Gaya da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin.
Sauran jiga-jigan siyasar da aka saka cikin kwamitin sun haɗa da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Bichi, Abubakar Kabir Bichi, da Sanatoci AbdulRahman Kawu Sumaila da Rufai Sani Hanga, tare da sauran manyan ’yan jam’iyyar APC da za su taimaka wajen jagorantar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a Kano a 2027.
