DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasaKotu ta sanya ranar sauraren ƙarar neman hana Tinubu takara

Kotu ta sanya ranar sauraren ƙarar neman hana Tinubu takara

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta sanya ranar 21 ga Satumba, 2026 domin sauraren ƙarar da ke neman hana Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 bisa zargin takardun shaida na bogi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wata ƙungiya ce mai suna Centre for Reform and Public Advocacy (CFRPA) ta shigar da ƙarar, inda ta nemi kotun ta hana Shugaba Tinubu shiga takarar zaɓen.

Ƙungiyar ta zargi Shugaba Tinubu da gabatar wa hukumar zaɓe Mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, takardun shaidar karatu da ta ce an ƙirƙira su daga Chicago State University, da kuma takardar shaidar NYSC da ta ce ta bogi ce, a lokacin zaɓen 2023.

Ƙarar mai lamba FHC/K/CS/312/2026 ta haɗa Shugaba Tinubu, INEC da Chicago State University a matsayin waɗanda ake ƙara. A cewar rahoton, ɓangarorin da ke cikin ƙarar sun riga sun gabatar da takardunsu gaban kotu kafin ranar 21 ga Satumba.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata