Shugaban rundunar sojin Uganda, Muhoozi Kainerugaba, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasar a zaɓen shekarar 2031, matakin da ya sake jawo hankalin jama’a kan batun wanda zai gaji mahaifinsa, Shugaba Yoweri Museveni, bayan kusan shekaru 40 yana mulkin ƙasar.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Kainerugaba mai shekaru 52 ya bayyana aniyar tasa ne cikin wasu saƙonni da ya wallafa a shafinsa na X, shekaru biyar kafin lokacin zaɓen.
Ya ce zai tsaya takarar “matsayi mafi girma a ƙasar” a shekarar 2031, yana mai cewa yana da yakinin za su samu nasara da yardar Allah.
Kainerugaba ya kuma bayyana cewa yana sa ran samun gagarumar nasara idan mahaifinsa ya mara masa baya, inda ya yi hasashen cewa zai samu kashi 90 cikin 100 na ƙuri’un zaɓen.
Wannan ba shi ne karo na farko da Kainerugaba ya nuna sha’awar neman shugabancin Uganda ba.
A baya ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaɓen watan Janairu, amma daga baya ya janye.
Maimakon haka, ya taka muhimmiyar rawa wajen yaƙin neman zaɓen mahaifinsa, inda ya mara wa Museveni baya har ya sake lashe zaɓen.
Shugaba Museveni mai shekaru 81 ya kasance shugaban Uganda tun shekarar 1986, kuma yana daga cikin shugabannin Afirka da suka fi dadewa a kan karagar mulki.
Sabuwar sanarwar ɗansa ta sake dawo da batun makomar jam’iyyar National Resistance Movement (NRM) da kuma wanda zai iya gaji Museveni idan ya bar mulki.
Kainerugaba ne ke jagorantar ƙungiyar siyasa ta Patriotic League of Uganda, kuma tsawon shekaru ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da ke da burin maye gurbin mahaifinsa.
Sai dai harkokin siyasar Kainerugaba da wasu kalamansa a kafafen sada zumunta sun sha jawo ce-ce-ku-ce, musamman sakonnin da ya taba wallafawa kan jagoran adawa Bobi Wine.
Bobi Wine ya bar Uganda zuwa Amurka a farkon shekarar nan, yana mai cewa yana fargabar lafiyarsa, yayin da wani jagoran adawa, Kizza Besigye, ke tsare tun shekarar 2024 kuma yake fuskantar shari’a kan zargin cin amanar ƙasa.
Gwamnatin Museveni ta kuma fuskanci zarge-zargen azabtarwa, sace mutane da tsare abokan hamayya ba bisa ka’ida ba, sai dai hukumomi sun musanta zarge-zargen.
A halin yanzu, gwamnatin Uganda ba ta tabbatar da cewa Museveni zai sake neman wani wa’adin mulki ba.
Mai magana da yawun gwamnati, Alan Kasujja, ya ce Shugaban ƙasa da jam’iyyar NRM ne za su yanke shawara idan lokaci ya yi.
Sanarwar Kainerugaba ta 2031 ta sake mayar da batun wanda zai gaji Museveni cikin muhimman batutuwan siyasar Uganda, duk da cewa Museveni har yanzu yana kan gaba wajen jagorancin NRM.
