Shugaban darikar Ƙadiriyya a nahiyar Afirka, Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Kabara, ya bayyana goyon bayan ƙungiyar ga aniyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sake tsayawa takara a karo na biyu a babban zaɓen 2027, biyo bayan naɗa Sanata Abdul’aziz Yari a matsayin babban daraktan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Sheikh Qaribullah ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a birnin Kano lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu ƙarƙashin jagorancin Sanata Yari.
Malamin ya bayyana cewa naɗin Yari ya ƙara ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin ƙungiyar Ƙadiriyya da tawagar kamfen ɗin, yana mai jaddada cewa sanatan ya kwashe fiye da shekaru 20 yana kiyaye kyakkyawar alaƙa da gidan.
Sheikh Qaribullah ya ce, “Sama da shekaru 20 muna tare da Abdul’aziz Yari, kuma a bayyane yake yana marawa wannan gida baya. Shi ɗan gida ne, kuma duk abin da ya zo da shi ba mu da wani zaɓi illa mu goya masa baya.”
Malamin ya ƙara da cewa ƙungiyar ba wai kawai tana goyon bayan sake zaɓen Tinubu ba ne, har ma ta yi imanin cewa shugaban yana da kyakkyawar manufa ga ƙasar Nijeriya. Ya kuma bayyana cewa ɗariƙar za ta fara gudanar da addu’o’i na musamman tare da ɗimbin mabiyanta domin samun zaman lafiya, farfaɗowar tattalin arziki, samar da ayyukan yi ga matasa, da kuma kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a ƙasar.
Sanata Yari, wanda ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje; James Faleke; Sanata Ali Modu Sheriff; Aminu Masari; Adamu Aliero; da sauran mambobin tawagar, ya bayyana cewa sun fara ziyarar neman goyon bayan ne daga wajen shugabannin addinai saboda girma da mutuncin da suke da shi a idon al’umma.
