Aƙalla mutum uku ne suka rasa rayukansu a cikin wani masallaci, yayin da wasu da dama da aka yi garkuwa da su, bayan da ƴan bindiga suka kai hari ƙauyen Tsamaye da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.
Mazauna ƙauyen sun shaida wa Daily Trust cewa maharan sun iso da ɗumbin yawa da misalin ƙarfe 8:30 na dare a ranar Talata, kuma sun ci gaba da hare-hare a ƙauyen har zuwa kusan ƙarfe 3:00 na daren ranar Laraba.
Rahotanni sun ce ƴan bindigar sun shafe sama da sa’o’i shida suna kai hare-hare kan mazauna ƙauyen, suna kwasar dabbobi, satar kayayyaki masu amfani tare da harba bindigogi ba ƙaƙƙautawa.
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya ce bayan maharan sun tsere, mazauna ƙauyen sun gano gawarwakin mutum bakwai a safiyar ranar Laraba.
Ya ce, “Muna zaune bayan sallar Isha’i ne sai ƴan bindigar suka mamaye ƙauyenmu. Da farko sun kewaye jami’an tsaro da ke bakin aiki a ƙauyen tare da bude musu wuta. Sun hana su fitowa daga inda suke, yayin da sauran maharan suka riƙa shiga gida-gida suna kwasar dabbobi, satar kayayyaki da kuma garkuwa da wasu.”
Majiyar ta ce mutum uku daga cikin waɗanda aka kashe sun mutu ne a cikin wani masallaci, inda ta ƙara da cewa dukkaninsu ƴan gudun hijira ne da suka tsere daga ƙauyukan da ke makwabtaka sakamakon yawaitar hare-haren ƴan bindiga.
Ya kuma bayyana cewa maharan sun kutsa cikin shaguna da dama, sun kwashe kayayyaki, sun ƙone wata mota tare da banka wa shaguna biyu wuta kafin su fice daga ƙauyen.
Majiyar ta ce zuwa lokacin haɗa rahoton ba a iya tantance adadin mutanen da aka yi garkuwa da su, domin mutane da dama sun tsere zuwa cikin dazuka yayin harin.
Ya ƙara da cewa maharan sun tafi da dabbobi masu yawa, sai dai ba a san adadinsu ba.
A cewarsa, mutum biyu daga cikin waɗanda aka kashe ƴan asalin ƙauyen Tsamaye ne, yayin da sauran mutum biyar ƴan gudun hijira ne daga ƙauyukan da ke makwabtaka waɗanda suka nemi mafaka a ƙauyen.
Har ila yau, ya ce an tabbatar da sace aƙalla mutum uku bayan da iyalansu suka kira wayoyinsu, inda ƴan bindigar suka amsa tare da tabbatar da cewa mutanen suna hannunsu.
Ya bayyana cewa jami’an tsaron da ke bakin aiki a ƙauyen sun gamu da harin ba tare da shiri ba, lamarin da ya bai wa ƴan bindiga damar kewaye su tare da hana su kai ɗauki ga mazauna ƙauyen.6
Da aka tuntubi kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufai, ya tabbatar da cewa rundunar ta samu rahoton faruwar lamarin, amma har yanzu tana jiran cikakkun bayanai kan abin da ya faru.
