Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta kama wani matashi mai shekaru 22, Sani Dikko, bisa zargin haɗa baki da wasu mutane biyu wajen yin garkuwa da kakansa, inda ya karɓi kuɗin fansa har Naira miliyan uku kafin a sake shi.
An kama Dikko tare da Kabir Sani, mai shekaru 22, da Salisu Bello, mai shekaru 22, a yayin wani samame da jami’an rundunar ta sashin yaƙi da manyan laifuka suka gudanar a yankin Marabar Shema da ke ƙaramar hukumar Dutsin-Ma.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Aliyu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a madadin Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Ali Fage.
DSP Abubakar Aliyu ya ce an kama mutanen uku ne a ranar 12 ga Satumba 2026, da misalin ƙarfe 8:23 na dare, yayin wani sintiri na ƙarfafa tsaro da jami’an rundunar ke gudanarwa bisa sahihan bayanan sirri.
A cewar rundunar, jami’an sashen yaƙi da manyan laifuka sun samu bayanan sirri kan wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane mai mutane uku, inda suka kai samame tare da cafke waɗanda ake zargin.
Rundunar ta bayyana Sani Dikko a matsayin wanda ya bayar da bayanan da suka kai ga gano su, yayin da Kabir Sani da Salisu Bello suke cikin waɗanda ake zargin suna da hannu a lamarin.
A yayin binciken farko, rundunar ta ce waɗanda ake zargin sun amsa cewa suna da hannu wajen aikata laifin da ake tuhumarsu da shi.
Musamman, rundunar ta ce Sani Dikko ya amsa cewa ya haɗa baki da sauran mutanen biyu wajen yin garkuwa da kakansa, Alhaji Lawal, kimanin makonni uku kafin a kama su.
A cewar sanarwar, Alhaji Lawal ya shafe kwanaki 16 a hannun masu garkuwa da shi kafin a sake shi bayan an biya kuɗin fansa har Naira miliyan uku.
Rundunar ta ce dukkan waɗanda ake zargin suna tsare a hannun jami’an tsaro yayin da ake ci gaba da bincike domin gano ƙarin bayanai da kuma gano ko akwai wasu mutane da ake zargin suna da hannu a cikin wannan ƙungiyar.
A wani ɓangare na aikin, rundunar ta kuma sanar da ceto wasu mata biyu da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a wani hari da suka kai ƙauyen Sha’iskawa Fulani da ke ƙaramar hukumar Kankia.
Matan da aka ceto su ne Assubi Rabe, mai shekaru 45, da Rabi Isyaku, mai shekaru 27.
Rundunar ta ce kimanin ’yan bindiga takwas ɗauke da makamai ne suka kai harin da misalin ƙarfe 12:45 na dare ranar 14 ga Satumba 2026, inda suka yi awon gaba da matan.
Bayan samun kiran neman agaji, jami’in ’yan sandan da ke kula da yankin Kankia ya gaggauta tattara jami’ai tare da tura su wurin da lamarin ya faru.
Jami’an sun yi musayar wuta da ’yan bindigan, inda rundunar ta ce ƙarfin wutar da jami’an suka nuna ya tilasta wa maharan tserewa zuwa cikin daji.
Hakan ya bai wa jami’an damar shiga wurin tare da ceto matan biyu cikin ƙoshin lafiya, a cewar sanarwar.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Katsina, CP Ali Fage, ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin bisa jarumtakarsu da ƙwarewarsu wajen tunkarar masu aikata laifuka.
CP Fage ya kuma jaddada aniyar rundunar na ci gaba da gudanar da ayyuka domin yaƙi da garkuwa da mutane da ayyukan ’yan bindiga a faɗin jihar.
Kwamishinan ya buƙaci al’ummar Katsina da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa domin taimaka musu wajen ɗaukar matakan da suka dace kan masu aikata laifuka.
