DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiSojoji sun ceto mutum 36 da aka yi garkuwa da su a...

Sojoji sun ceto mutum 36 da aka yi garkuwa da su a mako ɗaya

Dakarun sojin Nijeriya sun sami nasarar ceto mutum 36 da aka yi garkuwa da su tare da hallaka manyan shugabannin ‘yan ta’adda da dama a sabbin samamen da suka kai a sassan ƙasar nan.

Hedikwatar tsaron Nijeriya (DHQ) ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na ayyukan tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya fitar a ranar Asabar kan samamen da aka gudanar tsakanin 31 ga watan Agusta zuwa 3 ga watan Satumban 2026.

Janar Onoja ya ce ayyukan sun mayar da hankali ne kan ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, masu safarar makamai, da masu tada ƙayar baya a shiyyoyi daban-daban na ƙasar.

A yankin Arewa maso Gabas, dakarun rundunar Operation HADIN KAI sun kashe ‘yan ta’adda a Borno da Yobe tare da ƙwato makamai da bama-bamai na IED. Sun kuma kama mutumin da ya ke kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a Konduga, yayin da mata da ƙananan yara 21 suka miƙa wuya ga sojoji a Mafa bayan ɓarkewar faɗa tsakanin ɓangarorin ‘yan ta’addar.

A Arewa maso Yamma kuwa, dakarun Operation FANSAN YAMMA sun hallaka ƙasurguman ‘yan bindiga biyu a ƙauyen Kogo da ke ƙaramar hukumar Matazu a Katsina, sannan suka kama wata mota a Giwa da ke jihar Kaduna ɗauke da harsasai 793 a cikin buhun hatsi. Haka kuma a jihar Zamfara, sojoji sun yi wa ‘yan ta’adda kwanton-ɓauna a Kwanar Jolof da ke hanyar Shinkafi zuwa Zurmi inda suka kashe da yawa daga cikinsu tare da ƙwato bindigar kakkabo jirage ta RPG da sauran makamai.

A ɓangaren ceto mutane:

  • An ceto mutum 6 a Wasagu ta jihar Kebbi.

  • An ceto mutum 23 (maza 3 da mata 20) a yankin Wuya da ke ƙaramar hukumar Anka a jihar Zamfara bayan kwashe makwanni uku a tsare.

  • An ceto mutum biyu a kan hanyar Dandume zuwa Birnin Gwari a jihar Katsina.

  • Dakarun sun kuma ruguza sansanin ‘yan ta’adda a dajin Bilange da ke Tangaza a jihar Sokoto.

A yankin Tsakiyar Ƙasa, dakarun Operation WHIRL STROKE sun kashe ɗan bindiga ɗaya a Katsina-Ala ta jihar Benue, suka tilasta wa masu garkuwa barin mata biyu a dajin Agbodakodo a Kogi, sannan dakarun Operation SAVANNAH SHIELD suka ceto maza biyar a kan hanyar Kotonkoro zuwa Bangi a jihar Neja.

Babban hafsan tsaron ƙasar, Janar Olufemi Oluyede, ya jinjina wa sojojin bisa ƙoƙarinsu da kuma kyakkyawar haɗin gwiwar da ke tsakanin sojoji, ‘yan sanda, DSS, da ‘yan banga, yana mai tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ba za su sassauta ba har sai an dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a faɗin ƙasar.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata