Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa jihar za ta yi aiki domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a dukkan matakai na zaɓen 2027, tare da kira ga masu riƙe da muƙaman siyasa su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a da gina jam’iyyar.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da zaɓaɓɓun jami’an gwamnati da masu muƙaman siyasa a gidan gwamnatin Kano, kamar yadda mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana a wata sanarwa.
Gwamna Yusuf ya ce Kano za ta jagoranci sauran jihohi wajen samar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ƙuri’u masu yawa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yana mai cewa gwamnatinsa ba ta da nadamar goyon bayan shugaban ƙasar.
Gwamnan ya bayyana sake zaɓen Shugaba Tinubu a matsayin alhakin haɗin gwiwa na dukkan ‘yan jam’iyya da masu riƙe da muƙaman gwamnati.
Ya kuma umarci dukkan masu muƙaman siyasa da har yanzu ba su yi rajista da APC ba da su gaggauta yin hakan, yana mai cewa wajibi ne duk wani jami’in gwamnati ya kasance cikin jam’iyyar tare da taka rawa wajen ƙarfafa ta kafin zaɓe.
A cewarsa, gwamnatinsa za ta tabbatar APC ta samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna da na majalisun tarayya da jiha da kuma ƙananan hukumomi.
Gwamnati Ta Rabawa Masu Muƙaman Siyasa Filaye
A wani ɓangare na ƙarfafa gwiwar masu muƙaman siyasa, Gwamna Yusuf ya amince da rabon filaye ga sama da mataimaka 300 da suka haɗa da Manyan Mataimaka na Musamman da Mataimaka na Musamman da masu rahotanni na musamman da kuma mataimakan kansu.
Haka kuma ya amince da bai wa kowannensu tallafin naira 100,000.
Shugabannin APC Sun Bayyana Shirinsu Na 2027
Da yake jawabi a wajen taron, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Hon. Ismail Falgore, ya ce APC za ta ci gaba da tallata nasarorin gwamnatin Shugaba Tinubu a Kano.
Ya ce ayyukan mazabu da ‘yan majalisar dokokin jihar suka gudanar tare da goyon bayan gwamnan sun ƙara wa jam’iyyar karɓuwa a faɗin jihar.
Shi ma shugaban APC na Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa, ya bayyana cewa jam’iyyar ta shirya tsaf domin zaɓen 2027, yana mai cewa “an riga an ja zare” tsakaninsu da ƴan Kwankwasiyya.
A ƙarshen taron, jami’an gwamnati da masu muƙaman siyasa sun kaɗa ƙuri’ar amincewa da Shugaba Tinubu da Gwamna Yusuf, tare da alƙawarin ƙara zage damtse wajen yaɗa manufofin APC a matakin ƙasa da ƙasa.
