Manyan jam’iyyun siyasa a Nijeriya sun bayyana damuwa kan jinkirin sakin kudaden shirya zabukan 2027 ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, suna gargadin cewa hakan na iya kawo cikas ga shirye-shiryen zaben da kuma amincin tsarin dimokuradiyya.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, jam’iyyun ADC da PDP da kuma NDC sun ce jinkirin na iya shafar sayen kayan aiki, rage yarda da tsarin zabe a idon jama’a tare da kawo tarnaki ga gudanar da sahihin zabe a shekarar 2027.
DCL Hausa ta ruwaito cewa duk da damuwar da jam’iyyun suka nuna, INEC ta ce babu wata matsala ta rashin kudi da za ta dakatar da shirinta, tana mai cewa tuni ta fara wasu shirye-shiryen gudanar da zaben bisa tanadin dokar zabe.
INEC ta ce ba a sake kudade ba tukuna
A ranar Alhamis ne Kwamishinan INEC mai kula da wayar da kan masu kada kuri’a da hulda da jama’a, Mohammed Haruna, ya bayyana cewa har yanzu hukumar ba ta karbi kudaden kasafin zabukan 2027 ba.
Ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da cibiyar Peering Advocacy and Advancement Centre ta shirya a Abuja.
Sai dai Haruna ya ce duk da haka hukumar ta fara wasu shirye-shirye ciki har da sayen sababbin na’urorin BVAS domin maye gurbin wadanda suka lalace ko suka bace bayan zabukan baya.
Har ila yau, ya ce INEC na shirin gudanar da gwajin zaben shugaban kasa domin gwada tsarin fasahar ta da kuma kauce wa matsalolin da suka shafi IReV a zaben 2023.
Kasafin zaben 2027 ya haura biliyan N873
INEC ta nemi kasafin kudin da ya kai naira biliyan 873.78 domin gudanar da zabukan 2027, wanda ya hada da kudin gudanar da zabe da fasaha da kuma kayan aiki.
Masana harkokin zabe sun ce sakin kudade da wuri yana da muhimmanci saboda yawancin kayan zabe da fasahohin da ake amfani da su ana sayo su ne daga kasashen waje kuma suna bukatar lokaci kafin a kera su da jigilar su zuwa rumfunan zabe fiye da 176,000 da ke fadin Nijeriya.
Jam’iyyun adawa sun nuna damuwa
Sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce jinkirin na da hatsari saboda akwai kayayyaki masu yawa da INEC ke bukatar saya daga kasashen waje.
Ya ce, “Idan ba a fara sayen wadannan kayayyaki da wuri ba, hakan na iya zama barazana ga zaben.”
Shi ma Sakataren yada labarai na PDP karkashin kwamitin rikon kwarya na Tanimu Turaki, Ini Ememobong, ya ce jinkirin sakin kudade na iya zama wata hanya ta kawo cikas ga tsarin zabe.
Ya ce zabe yana da jadawalin lokaci mai tsauri wanda bai kamata a yi wasa da shi ba, yana mai kira ga Majalisar Tarayya da bangaren zartarwa su tabbatar an bai wa INEC kudaden da take bukata cikin lokaci.
Mataimakin Sakataren yada labarai na NDC, Abdulmumin Abdulsalam, shi ma ya bayyana damuwa amma ya ce yana sa ran gwamnati da majalisa za su dauki matakin da ya dace kafin lamarin ya rikide zuwa babbar matsala.
APC ta ce babu abin damuwa
Jam’iyyar APC mai mulki ta yi watsi da zargin cewa jinkirin kudaden zai kawo matsala ga zaben 2027.
Mataimakin Sakataren yada labarai na jam’iyyar, Duro Meseko, ya ce APC na da cikakken yarda da shugabancin INEC karkashin Farfesa Joash Amupitan.
Ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai gaza cika nauyin da kundin tsarin mulki ya dora masa ba wajen tabbatar da gudanar da sahihin zabe.
Meseko ya kuma ce INEC ta riga ta fara tallata kwangilolin sayen kayayyakin zabe, abin da ke nuna cewa shirye-shiryen zaben na tafiya yadda ya kamata.
Yiaga Africa ta yi gargadi
Memba a kwamitin amintattu na Yiaga Africa, Farfesa Nnamdi Aduba, ya gargadi cewa duk wani jinkiri wajen bai wa INEC kudade na iya jefa sahihancin zaben 2027 cikin hadari.
Ya ce zabe na bukatar dogon shiri da sayen kayan aiki da jigilar su cikin lokaci, yana mai cewa rashin sakin kudade da wuri na iya bude kofar tasirin siyasa da lalata tsarin zabe.
INEC ta ce shirye-shirye na tafiya yadda ya kamata
Wani babban jami’in INEC da ya yi magana ba tare da bayyana sunansa ba, ya ce tsarin sakin kudaden zabe ana yin sa ne a matakai ba lokaci guda ba.
Ya ce gwamnatin tarayya na ba wa hukumar goyon baya kuma shirye-shiryen sayen kayayyaki da bunkasa fasaha na tafiya yadda ya kamata ba tare da wata matsala ba.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa zabukan shugaban kasa da na majalisar dokoki za su gudana ne a ranar 16 ga Janairun 2027, yayin da zabukan gwamnoni da majalisun jihohi za su gudana ranar 6 ga Fabrairun 2027.
