Ɗan takarar jam’iyyar APC, Injiniya Usman Maijama’a Kallamu, ya lashe zaɓen cike gurbi na mazaɓar tarayya ta Gombe/Kwami/Funakaye da aka gudanar a ranar Asabar, 19 ga watan Satumban 2026.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kallamu ya samu ƙuri’u 41,121 inda ya kayar da sauran ‘yan takara huɗu da suka fafata a zaɓen da aka gudanar domin cike gurbin kujerar da ta rage a majalisar wakilai ta ƙasa.
Wannan kujera ta zama fayau ne biyo bayan rasuwar ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar a baya, marigayi Hon. Yaya Bauchi Tongo.
Yayin da yake sanar da sakamakon zaɓen a ranar Lahadi, baturen zaɓe na mazaɓar, Farfesa Umar Gurama, ya ayyana Kallamu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara bayan ya samu mafi yawan ƙuri’un da aka kaɗa.
Farfesa Gurama ya ce, “Adadin dukkan ƙuri’un da aka kaɗa ya kai 47,301, yayin da adadin sahihan ƙuri’u ya kasance 46,551. Ƙuri’un da suka lalace kuma guda 750 ne.”
Bisa sakamakon da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar, jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 41,121, sai jam’iyyar Labour Party (LP) da ta samu ƙuri’u 3,553. Jam’iyyar APM ta samu ƙuri’u 872, jam’iyyar NDP ta samu ƙuri’u 707, yayin da jam’iyyar APP ta tashi da ƙuri’u 298.
An gudanar da zaɓen ne a runfunan zaɓe guda 903 da ke cikin gundumomi 31 a ƙananan hukumomin Gombe, Kwami, da Funakaye.
Sakamakon wannan nasara da ya samu, Injiniya Kallamu ne zai wakilci mazaɓar tarayya ta Gombe/Kwami/Funakaye a majalisar wakilai domin kammala ragowar wa’adin mulkin da ake ciki.
