Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ya buƙaci ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, da ya fayyace wa ‘yan Nijeriya cikakken bayanin doka da na kasafin kuɗi game da shirinsa na dawo da tallafin man fetur ta hanyar tallafa wa matatun cikin gida.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kwamitin, Dr. Dele Alake, ya fitar a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumban 2026, ya bayyana cewa shawarar da Atiku ya sake nanatawa a Abuja kan bai wa matatun mai na cikin gida tallafi domin saukar da farashin fetur da dizal na haifar da manyan tambayoyi na doka da tattalin arziki da ya kamata ya amsa.
Alake ya bayyana cewa sashi na 205(1) na dokar masana’antar man fetur (PIA) ta shekarar 2021 ya tanadi cewa ‘yancin kasuwa ne kaɗai zai riƙa kayyade farashin kayayyakin man fetur, inda hukumar kula da harkokin man fetur ta NMDPRA ta riga ta bayyana cewa ba ita ke sanya farashin mai a yanzu ba. Don haka kwamitin ya buƙaci Atiku ya yi bayanin ko matatun man da za su karɓi tallafin za a tilasta musu sayar da mai a kan farashin da gwamnati ta kayyade, da kuma dokar da za a yi amfani da ita wajen yin hakan ba tare da an saɓa wa dokar PIA ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “dole ne Atiku ya bayyana adadin kuɗin da shirin zai lashe da kuma yadda zai samar da su. Rage farashin ɗanyen mai ga matatun cikin gida zai rage kudaden shiga da ke shiga asusun tarayya, wanda zai iya mayar da ƙasar cikin matsalar rashin biyan albashi ga jihohi kamar yadda ya faru kafin zuwan gwamnatin Tinubu a 2023.”
Kwamitin na APC ya ƙiyasta cewa irin wannan tallafi na iya lakume tsakanin naira tiriliyan 17 zuwa tiriliyan 21 a duk shekara. Ya kuma zargi Atiku da sauya matsayarsa ta baya, inda a shekarar 2022 a Makarantar Kasuwanci ta Legas (LBS) ya bayyana tallafin mai a matsayin zamba tare da yin alƙawarin cire shi gaba ɗaya, amma a yanzu yake neman dawo da shi.
A maimakon komawa ga tsarin tallafi da ke jawo fasa-ƙwauri da tarin basussuka, sanarwar ta ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta mayar da hankali ne kan samar da hanyoyin sufuri masu sauƙi ta hanyar amfani da iskar gas ta CNG da motocin lantarki, inda tuni aka canza motoci sama da 120,000 zuwa tsarin CNG wanda hakan ya rage kuɗin mota a jihohi daban-daban tsakanin kashi 31 zuwa 83 cikin 100.
Kwamitin ya buƙaci Atiku da ya karanta dokar PIA da kyau sannan ya fitar da cikakkiyar takarda mai ƙunshe da tsarin doka da kasafin kuɗin shawarar tasa, maimakon yin alƙawuran da ba su da tabbas.
