DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeLabaraiTinubu ya tura Shettima ya waƙilce shi a babban taron UNGA

Tinubu ya tura Shettima ya waƙilce shi a babban taron UNGA

Bayan shafe makonni ana ce-ce-ku-ce, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa ba zai samu damar halartar zama na 81 na babban taron majalisar ɗinkin duniya (UNGA) da za a gudanar a birnin New York na ƙasar Amurka ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an fara hasashen rashin halartar shugaban ne bayan da fadar shugaban ƙasa ta sanar da cewa Tinubu zai dawo gida Nijeriya bayan kammala hutunsa na makonni uku a nahiyar Turai.

Tun da farko dai, wakilin Nijeriya na dindindin a majalisar ɗinkin duniya, Jimoh Ibrahim, ya bayyana cewa Tinubu zai halarci taron na UNGA na 81, har ma ya ƙara da cewa an tanadi wurin zama kusa da takwaransa na Amurka, Donald Trump, sai dai fadar shugaban ƙasar ta yi gum game da batun halartar tasa.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha, ya fitar a ranar Lahadi, ya sanar da cewa Shugaba Tinubu ya umarci mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, da ya wakilce shi tare da jagorantar tawagar Nijeriya zuwa babban taron.

Sanarwar ta ce: “Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da ya wakilce shi tare da jagorantar tawagar Nijeriya zuwa zama na 81 na babban taron majalisar ɗinkin duniya (UNGA) a New York, ƙasar Amurka.”

Shettima zai jagoranci babbar tawaga da ta haɗa da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara; gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal; ministoci; da sauran manyan jami’an gwamnatin tarayya.

Babban zauren mahawara na taron zai gudana ne daga ranar 22 zuwa 28 ga watan Satumban 2026, ƙarƙashin taken nan mai cewa, “Maido da yarda, tafiyar da sauye-sauye: Majalisar ɗinkin duniya mai aiki domin kowa.”

A yayin mahawarar, Sanata Shettima zai gabatar da jawabin Nijeriya inda zai bayyana matsayar ƙasar da muhimman abubuwan da ta sanya a gaba kan batutuwan da suka shafi ci gaban ƙasa, zaman lafiya da tsaro, haɓakar tattalin arziki, da haɗin gwiwar ƙasashe.

Haka kuma zai halarci tarurruka na musamman kan ci gaba, sauyin yanayi, da ganawa da shugabannin ƙasashe da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa domin ƙarfafa diflomasiyyar tattalin arzikin Shugaba Tinubu.

Wannan ne karo na uku a jere da Shugaba Tinubu ba zai halarci babban taron majalisar ɗinkin duniya ba tun bayan hawan sa mulki a shekarar 2023.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata