DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeSiyasa'Ba zan je hutu ƙasashen ƙetare ba idan aka zaɓe ni a...

‘Ba zan je hutu ƙasashen ƙetare ba idan aka zaɓe ni a 2027’

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi alƙawarin cewa ba zai taɓa fita zuwa hutu a ƙasashen ƙetare ba idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa, inda ya bayyana cewa zai riƙa amfani da lokutan hutu domin ziyartar sassan ƙasar nan da ke fuskantar matsalar tsaro.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Obi ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wani taron tattaunawa da al’umma (town hall meeting) da aka gudanar a garin Kaduna, inda ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ba da fifiko na musamman wajen garambawul ga tsarin tsaron ƙasar.

“Kuma bari na ba ku tabbaci, a cikin shekaru huɗu, ba zan taɓa yin  hutu a wajen wannan ƙasa ba. Idan zan ɗauki rana guda hutu, zan yi ta ne a Zamfara, Borno, ko Kano. Zan yi ta a Oyo ko Ondo. Haka ya kamata ya kasance.”

Ɗan takarar ya bayyana cewa ya kamata ‘yan Nijeriya su samu damar yin tafiye-tafiye a faɗin ƙasar cikin ‘yanci ba tare da tsoron sace su domin neman kuɗin fansa ba. Ya ƙara da cewa a lokutan baya ya sha tuƙin mota daga Legas zuwa Kaduna da sauran wurare, don haka ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta kawo ƙarshen wannan matsala.

Haka kuma, Obi ya yi alƙawarin aiwatar da manufofin da za su buɗe wa kowane yaro da matashi damammaki ba tare da la’akari da asalin danginsa ko talaucin iyayensa ba, yana mai cewa, “muna son manufofin da kowane yaro zai samu damar zuwa makaranta, ƙasar da ‘ya’yan talakawa za su iya zama wani abu a rayuwa ba tare da sai sun san wani a gwamnati ba.”

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata