Fursunoni biyu sun rasa rayukansu biyo bayan ɓarkewar cutar kwalara a cibiyar ajiya da gyaran hali ta Kurmawa da ke Jihar Kano.
Hukumar gyaran hali ta Nijeriya (NCoS) ce ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Kakakin hukumar, JN Osuji, ya bayyana cewa sakamakon binciken dakin gwaje-gwaje da aka gudanar a ranar 23 ga Satumba ya tabbatar da ɓarkewar cutar, bayan an fara samun alamunta a jikin wani fursuna a ranar 17 ga Satumba wanda ya fara amai da zawo.
Osuji ya bayyana cewa an kwantar da fursunan nan take a asibitin gidan yarin tare da ba shi magani, inda washegari aka kaddamar da matakan gaggawa na kiwon lafiya tare da hadin gwiwar hukumomin lafiya na Jihar Kano.
A cewar sanarwar, mutum biyu ne suka rasu sakamakon cutar—ɗaya a cikin cibiyar gyaran halin, ɗayan kuma a babban asibitin kula da cututtuka masu yaɗuwa na Jihar Kano.
Shugaban Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa, Sylvester Nwakuche, ya ba da umarnin ci gaba da bayar da kulawar lafiya, sa-ido, da kuma daukar matakan kariya tare da haɗin gwiwar gwamnatin Jihar Kano. Haka kuma ya tura tawagar manyan jami’an lafiya daga hedkwatar hukumar da ke Abuja zuwa cibiyar domin ci gaba da sanya ido.
Hukumar ta NCoS ta bayyana cewa an samu nasarar shawo kan cutar, inda ta tabbatar da cewa ba a sake samun karin wani fursuna da ya mutu ba tun bayan tabbatar da bullar cutar. Ta kuma buƙaci al’umma da su riƙa dogaro da sahihan bayanai daga mahukunta.
