Gwamnatin Nijeriya ta kashe zunzurutun kuɗi har naira tiriliyan 7.7 wajen biyan kuɗin ruwan bashi a rabin farko na shekarar 2026, adadin da ya kai kashi 124.2 cikin 100 na dukkan jimillar kuɗaɗen shigar da gwamnati ta samu a wannan lokaci, wanda ya tsaya a naira tiriliyan 6.2.
Wannan ƙididdiga na ƙunshe ne a cikin sabon rahoton Bankin Duniyana watan Oktoba, 2026 mai taken Nigeria Development Update, wanda ya nuna cewa kuɗin ruwan bashin kaɗai ya zarce jimillar kuɗaɗen shigar gwamnatin da naira tiriliyan 1.5 a cikin watanni shida na farkon shekara (Janairu zuwa Yuni).
Rahoton ya bayyana cewa kuɗin ruwan bashin ya ƙaru da naira tiriliyan 2.1 (ƙaruwar kashi 37.5 cikin 100) idan aka kwatanta da naira tiriliyan 5.6 da aka biya a makamancin wannan lokaci a shekarar 2025. Bankin ya bayyana cewa tsadar karɓar lamuni a cikin gida (high domestic borrowing costs) ita ce babban dalilin da ya haddasa wannan ƙaruwa.
Duk da cewa jimillar kuɗin shigar gwamnatin tarayya ta ƙaru da kashi 72.2 cikin 100—daga naira tiriliyan 3.6 a shekarar 2025 zuwa naira tiriliyan 6.2 a 2026 sakamakon ƙaruwar kudaden shigar man fetur da harajin kamfanoni—kuɗaɗen da gwamnatin ke kashewa sun ƙaru sosai, inda suka kai naira tiriliyan 16.1.
Haka kuma, rahoton ya nuna cewa yayin da aka kashe naira tiriliyan 4.2 wajen biyan albashin ma’aikata sakamakon ƙarin albashi, kuɗaɗen da aka ware domin manyan ayyukan raya ƙasa sun ragu ƙwarai zuwa naira biliyan 700 kacal. Wannan na nufin cewa gwamnatin tarayya ta kashe kuɗi har sau 11 wajen biyan ruwan bashi fiye da abin da ta kashe a manyan ayyukan raya ƙasa.
Bankin Duniya ya buƙaci Gwamnatin Nijeriya da ta taƙaita ciyo bashi mai tsadar ruwa, ta mayar da hankali kan basussuka masu sauƙi, tare da ƙara ƙaimi wajen tara kuɗaɗen shiga domin magance wannan ƙalubale da ke shafar ci gaban ƙasa.
