Kwanaki 150 bayan da ’yan ta’adda suka sace ɗalibai 78 a Jihar Borno, iyayen yaran sun tsinci kansu a cikin mawuyacin halin da ya tilasta musu ɗage zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja saboda matsananciyar talauci da rashin kuɗin mota.
Iyayen sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa sun ɗage wannan tafiya ne sakamakon rashin kuɗin kuɓutar da kansu a babban birnin tarayya, rashin kuɗin mota, da kuma gaza samun abincin da za su bar wa sauran iyalansu a gida yayin gudanar da zanga-zangar.
Waɗannan yara na ci gaba da zama a hannun maharan ne bayan harin garkuwa da mutane daban-daban guda biyu da aka kai a ƙaramar hukumar Askira-Uba ta Jihar Borno, inda aka sace ɗalibai 42 a garin Mussa a ranar 15 ga Mayu, sannan aka kwashe wasu ɗaliban kwaleji 36 a garin Lassa a ranar 29 ga Yuni, 2026.
Shugaban kungiyar iyayen yara da aka sace, Ishaku Suya, ya bayyana cewa a baya sun bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki shida domin ta ceto ‘ya’yansu, amma wa’adin ya cika ba tare da an ji ɗuriyar gwamnatin ba. Ya ƙara da cewa a halin yanzu da yawa daga cikin iyalan suna ƙoƙarin girbe amfanin gonakinsu ne domin tara kuɗin motar zuwa Abuja.
“Dole ne mu tsara abin da kyau. Muna buƙatar isassun kuɗin da za mu bar wa iyalanmu abinci a gida da kuma waɗanda za mu kashe a Abuja, saboda ba za mu dawo ba har sai Shugaban Ƙasa ya saurare mu,” in ji Ishaku Suya.
A ɓangare guda, wasu daga cikin iyayen sun nuna ɓacin ransu kan yadda suka ce gwamnatin na nuna wariya wajen kuɓutar da mutane.
Sun kafa misali da yadda aka ceto sama da ɗalibai da malamai 40 da aka sace a ƙaramar hukumar Oriire ta Jihar Oyo cikin kwanaki 56 kacal bayan an tura dakarun soji na musamman da jiragen leƙen asiri, amma na Borno an kwashe kusan watanni biyar ba a ɗauki irin wannan mataki ba.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Human Rights Writers Association of Nigeria (HURIWA) ƙarƙashin jagorancin Kwamared Emmanuel Nnadozie Onwubiko ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta ɗaukar mataki na ceto yaran da ke cikin tsaka mai wuya.
