DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, October 12, 2026
HomeLabaraiYarjejeniyar kiwon lafiya ta $5bn tsakanin Nijeriya da Amurka na fuskantar suka

Yarjejeniyar kiwon lafiya ta $5bn tsakanin Nijeriya da Amurka na fuskantar suka

Wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) ta fannin kiwon lafiya mai darajar dala biliyan biyar da aka kulla tsakanin Gwamnatin Nijeriya da Amurka ta haifar da zazzafar muhawara, biyo bayan bayyanar da shugaban Ghana, John Dramani Mahama ya yi cewa ƙasarsa ta yi watsi da irin wannan yarjejeniya saboda fargabar take haƙƙin mallakar bayanan sirri na kiwon lafiyar ‘yan ƙasarta.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yarjejeniyar, wadda aka sanya wa hannu a ranar 19 ga Disamba, 2025 tsakanin ministan lafiya da jin daɗin jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, da Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard M. Mills Jr., ta buƙaci Nijeriya ta riƙa miƙa bayanan sakamakon binciken lafiya da samfuran ƙwayoyin cututtuka ga gwamnatin Amurka.

A ƙarƙashin tsarin mai ɗauke da manufar “America First Global Health Strategy”, Amurka za ta bayar da tallafin dala biliyan 2.1 yayin da Nijeriya za ta fitar da dala biliyan uku domin daƙile cututtukan kanjamau (HIV/AIDS), tarin fuka (TB), zazzabin cizon sauro (malaria), shan-inna (polio), da lafiyar mata da ƙanana yara.

Sai dai kuma, ƙwararrun likitoci da masu fashin baƙi kan bayanan sirri a Nijeriya sun soki Sashe na 5 na yarjejeniyar, wanda ya bayyana cewa ko da Nijeriya ta soke wannan yarjejeniya a nan gaba, hakan ba zai hana Amurka ci gaba da amfani da samfuran kwayoyin cututtukan da bayanan da aka riga aka ba ta ba.

Tsohon Shugaban Ƙungiyar Likitocin Nijeriya (NMA), Farfesa Innocent Ujah, da Dokta Rotimi Adesanya sun bayyana cewa bai kamata a bar wata ƙasa ta ci gaba da riƙe bayanan sirri bayan an soke yarjejeniya ba, domin hakan na iya zama barazana ga tsaron ƙasa.

Haka kuma, masani kan tsaron bayanan sirri, Dokta Olumide Babalola, ya gargaɗi cewa tsarin na iya keta dokar kare bayanan sirri ta Nigeria Data Protection Act 2023.

A ɓangaren siyasa, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ta bakin daraktan sadarwarsa Phrank Shaibu, ya buƙaci gwamnatin tarayya ta gaggauta wallafa cikakken bayanin yarjejeniyar a fili domin al’umma su gani, tare da nuna shakku kan yadda gwamnatin da ta gaza sakin kasafin ayyukan raya ƙasa na ma’aikatar lafiya a 2025 za ta iya fitar da dala biliyan uku na kason da ke kanta.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata