DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, October 12, 2026
HomeLabarai'Ku nemi hanyoyin samun kudi ba alawee ba kawai'

‘Ku nemi hanyoyin samun kudi ba alawee ba kawai’

Babban darakta na hukumar yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ya buƙaci matasa masu yi wa ƙasa hidima da su faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shigarsu, yana mai gargaɗin cewa dogaro da hanya guda ɗaya kawai ba zai ishe su wajen biyan buƙatun yau da kullum ba.

Birgediya Janar Nafiu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 12 ga Oktoba, 2026, yayin da yake jawabi ga masu yi wa ƙasa hidima na rukunin 2026 Batch ‘C’ Stream 1 a sansanin horon da ke Jihar Anambra, kamar yadda hukumar ta sanar a shafinta na X.

Shugaban ya shawarci matasan da su yi amfani da wannan shekara ta hidima wajen koyon sana’o’i masu amfani, gina tunanin kasuwanci, da kuma rungumar hanyoyin samun kuɗi na halal domin inganta rayuwarsu.

“Ku buɗe idanunku, ku yi abota, sannan ku yi amfani da damar da kuke da ita. Ku sayi hannun jari domin zuba jari na dogon lokaci,” in ji Nafiu.

Ya kuma buƙaci matasan da su jajirce wajen koyon dabarun sana’o’i daban-daban a lokacin da suke da sauran ƙuruciya, tare da bayar da gudunmawa mai ma’ana ga al’ummomin da aka tura su ta hanyar aikin koyarwa da ilimantarwa.

A nata ɓangaren, Jami’ar Kula da NYSC a Jihar Anambra, Misis Pauline Ojisua, ta bayyana cewa an yi wa masu yi wa ƙasa hidima 1,623 rajista a sansanin, tana mai yaba wa ɗabi’unsu nagari, biyayya, da goyon bayan da suke bayarwa wajen gudanar da ayyukan sansanin cikin nasara.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata