Ƙungiyar manyan ma’aikatan mai da iskar gas ta Nijeriya (PENGASSAN) ta bayyana cewa muhawara kan ko a cire tallafin man fetur ko a bar shi ta riga ta wuce lokaci, inda ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar da cewa alfanun matakin ya fara bayyana a rayuwar talakawan Nijeriya.
Tashar talabijin ta Channels ta ruwaito cewa shugaban ƙungiyar ta PENGASSAN, Bosun Olabiyi-Agoro, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin da yake magana a shirin The Morning Brief, a daidai lokacin da ake ƙara samun zafafan muhawara kan batun gabanin zaɓen 2027.
“Ina ganin lokacin muhawara kan batun cire tallafi ko rashin cire shi ya wuce. Mun riga mun yi hakan, amma abin da muke buƙata a yanzu shi ne mu fara ganin alfanun cire tallafin man fetur a rayuwar talakawan Nijeriya,” in ji Olabiyi-Agoro.
Ko da yake ya amince cewa matakin cire tallafin ya jefa ma’aikata da ‘yan ƙasa cikin matsanancin hali na tsawon shekaru uku da suka gabata, Olabiyi-Agoro ya ce duk da ƙaruwar tattalin arziƙin ƙasar (GDP) da kashi 4.43 a zangon farko na 2026, ya kamata a ce waɗannan alƙaluma sun sauya zuwa abinci da sauƙin rayuwa a ƙasa ba wai a takarda kawai ba.
Shugaban ƙungiyar ya ƙara da cewa cire tallafin ya taimaka wajen wadatar man fetur a ƙasar ba tare da an kashe kuɗin gwamnati ba, inda ya bayyana cewa ƙungiyar a shirye take ta bayar da tata gudunmawar ga kowace gwamnati domin ganin sauye-sauyen sun amfani talaka kai-tsaye.
